Kotu Ta Dauki Mataki Kan Tsohon Gwamnan da Ake Tuhuma da Wawushe N4bn

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Tsohon Gwamnan da Ake Tuhuma da Wawushe N4bn

  • A ranar Laraba, 24 ga watan Janairu aka fara sauraron ƙarar da aka shigar kan tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano
  • Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Bayan fara sauraron ƙarar, alƙalin kotun ya bayar da belin Obiano tare da ɗage ƙarar har zuwa ranar 4 ga watan Maris 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja – Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bayar da belin Willie Obiano, tsohon gwamnan jihar Anambra.

Kotun ta bayyana cewa Obiano na ƙarƙashin ikon ne kotun sannan ta umarci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa ta EFCC da ta ajiiye takardun tafiye-tafiyen wanda ake ƙara a hannun magatakardan kotun.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar dokoki ya aike da saƙo na musamman kan nasarar gwamnan arewa a Kotun Ƙoli

Willie Obiano ya samu beli
Kotu ta ba da belin Willie Obiano Hoto: Twitter
Asali: UGC

Mai shari’a Ekwo ya umurci magatakardan kotun da ya sanar da hukumar shige da fice ta Najeriya halin da ake ciki, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obiano Ya Gurfana Gaban Kotu

A ranar Laraba ne dai, Obiano ya gurfana a gaban kotun, inda ya musanta aikata tuhume-tuhume tara da hukumar EFCC take yi masa a gaban kotun, rahoton Arise tv ya tabbatar.

Lauyan mai shigar da ƙara, Slyvanus Tahir, (SAN), ya buƙaci kotun da ta tsare tsohon gwamnan.

Sai dai lauyan Obiano, Onyinyechi Ikpeazu ya bukaci kotu ta bayar da belin wanda yake karewa.

Da yake yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen, Ekwo ya yanke shawarar bayar da belin wanda ake ƙara bisa sharuɗɗan da EFCC ta gindaya a baya

Yanzu dai an dage sauraron shari’ar, inda aka sanya ranakun 4, 5, 6, da 7 ga watan Maris domin ci gaba da sauraronta.

Kara karanta wannan

An Kama Shugaban Ƙaramar hukuma da wani bisa hannu a yunkurin kashe kakakin majalisa a Arewa

EFCC Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Muazu Babangida

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun jihar Neja, ta yanke na wanke tsohon gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar.

EFCC dai tana tuhumar tsohon gwamnan ne da laifin karkatar da N4bn lokacin da yake kan ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng