Kano: Abba Ya Fadi Dalilin Fifita Bangaren Ilimi da Ware Kudade Ga Kwalejin Kwankwaso da Sauransu

Kano: Abba Ya Fadi Dalilin Fifita Bangaren Ilimi da Ware Kudade Ga Kwalejin Kwankwaso da Sauransu

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin ware makudan kudade a bangaren ilimi na kasafin kudin shekarar 2024
  • Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne don inganta bangaren ilimi kamar yadda gwamnan ya yi alkawari a yakin neman zabe
  • Za a raba kudaden don ayyuka tsakanin ma'aikatar ilimi mai zurfi da Kwalejin Rabiu Kwankwaso da Jami'ar Dangote da sauransu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin karkatar da makudan kudade bangaren ilimi.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare a jihar, Musa Sulaiman Shanono ya ce Gwamna Abba Kabir ya bai wa bangaren fifiko don inganta ilimi.

Abba Kabir ya bayyana dalilin fifita bangaren ilimi a kasafin kudin 2024
Bangaren ilimi ya tashi da kaso 28 a kasafin kudin 2024. Hoto: Abba Kabir.
Asali: Twitter

Mene dalilin fifita bangaren ilimi a Kano

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta yi martani kan kalaman batanci ga Usman Dan Fodiyo, ta ba da shawara ga jama'a

Shanono ya ce saboda yadda Abba Kabir ya himmatu wurin inganta ilimi shiyasa ya ware makudan kudade a bangaren fiye da sauran bangarori.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kudaden da aka ware wa bangaren ilimi shi ne mafi yawa idan akwa kwatanta da sauran bangarori a kasafin kudin 2024.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin kasafta kasafin kudin 2024 a jiya Talata 23 ga watan Janairu a Kano, cewar Daily Trust.

Bangarorin da za su mori kudaden a Kano

Ya ce:

"Gwamnatinsa ta shirya kara kasafin kudin a bangaren ilimi a ko wace shekara don inganta al'umma.
"Tun farkon hawan mu mulki, mun inganta bangaren ilimi tun daga firamare zuwa sakandare har gaba da haka.
"Don tabbatar da haka, an ware biliyan 125 wanda ya kai kaso 28.78 na kasafin kudin 2024 ga bangaren ilimi kadai."

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan sahihancin kasafin kudi da 'yan majalisun jihar PDP suka amince, akwai aiki

Daga kasafin kudin 2024, za a raba kudaden ne tsakanin Ma'aikatar ilimi mai zurfi da Kwalejin Rabiu Kwankwaso da Jami'ar Aliko Dangote.

Sauran sun hada da Jami'ar Yusuf Maitama Sule da Kwalejin Aminu Kano da Sa'adatu Rimi da sauransu, Latest News ta tattaro.

Dattawan APC a Kano sun shawarci Tinubu

A wani labarin, Dattawan jami'yyar APC a Kano sun bai wa Shugaba Tinubu shawara kan korar Umar Ganduje.

Wannan na zuwa ne bayan wasu matasan APC sun bukaci shugaban ya kori Ganduje saboda rashin katabus a zaben jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.