Ba mu da hannu cikin harin Benuwe, Inji kungiyar Miyetti Allah

Ba mu da hannu cikin harin Benuwe, Inji kungiyar Miyetti Allah

- Shugaban kungiyar, Alh. Bello Abdullahi Bodejo ya ce duk wani makiyayi da aka samu da bindigar AK47 ba dan kungiyar su bane

- Bodejo ya ce Fulani basu da dalilin da zai sa su tayar da hankali kan dokar hana kiwon domin sun shigar da kara kotu

- Bodejo kuma ya yi kira ga hukumomin tsaro su zage dantse wajen binciko masu kai hare-haren domin al'umma su dena zargin mambobin kungiyar

Shugaban kungiyan Fulani, Miyetti Allah Kautal Horre na kasa, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ya nisanta kungiyar da mambobin ta daga hare-haren da aka kai a Benuwe da ma sauran sassan Najeriya, inda ya bayyana cewa duk wani makiyayi da aka samu sauke da bindiga kirar AK47 ba bafilatani bane.

Ba mu da hannu cikin harin Benuwe, Inji kungiyar Miyetti Allah
Ba mu da hannu cikin harin Benuwe, Inji kungiyar Miyetti Allah

Abdullahi Bodejo ya yi wannan kiran ne jiya a Kano yayin da ya kira taron manema labari jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Saudiyya. Bodejo kuma ya yi tir da masu aikata wannan danyen aikin.

KU KARANTA: Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

Ya yi kira ga hukumomin tsaro su zurfafa bincike domin gano wadanda ke aikata wannan danyen aiki domin a al'umma su dena daganta makiyaya fulani da kashe-kashen da suke faruwa domin a cewarsa wasu miyagun ne ke amfani da kayan fulani suna yin barna.

Ya kara da cewa al'umman Fulani ba su da dalilin tada hankali a kan dokan hana kiwo a fili da gwamnatin Jihar Benuwe ta kafa domin tuni kungiyar ta su ta shigar da kara a kotu don nuna kin amincewar ta ga dokan.

Daga karshe Bodejo ya yi kira da Gwamnatin Tarayyah ta saka baki cikin al'amarin domin a shawo kan Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya janye dokar saboda makiyaya Fulani su sami damar walawa kamar yadda kowane dan kasa ke da ikon hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164