Ayarin Motoccin Mataimakin Gwamnan Sokoto Ta Yi Hatsari, An Rasa Rayyuka

Ayarin Motoccin Mataimakin Gwamnan Sokoto Ta Yi Hatsari, An Rasa Rayyuka

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Sokoto - Akalla mutane biyu ne suka rasu a ranar Laraba da yamma lokacin da ayarin motoccin Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Idris Gobir, ta yi hatsari a jihar.

Wata majiya wacce ta yi magana da wakilin jaridar Punch kan lamarin ta ce hatsarin ya yi sanadin rasuwar dan sanda da mai daukan hoto, Buhari Tanko.

Tawagar motoccin mataimakin gwamnan Sokoto ta yi hatsari
Mutane biyu sun mutu a hatsarin mataimakin gwamnan jihar Sokoto.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

"Yanzu na tabbatar da afkuwar lamarin, duk da bana tare da su lokacin da hatsarin ya faru.
"Na tabbatar cewa motar da ta yi hatsari ta yan sanda ne kuma mai daukan hoton na ciki tare da su a motar lokacin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

"Na gano cewa mutane biyu, dan sanda wanda ba zan iya tabbatar da sunansa ba da kuma mai daukan hoto, Buhari Tanko, sun mutu nan take. Abin bakin ciki ne da takaici."

A bangare guda, an rahoto cewa gwamnan jihar, Ahmed Sokoto, tare da mataimakinsa sun jagoranci wani dan jam'iyya zuwa Sabon Birni don halartar wani aiki.

Rundunar yan sanda sun tabbatar da lamarin

Da ya ke tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa'i, ya ce lamarin ya ritsa da wani direban mota cikin ayarin motoccin mataimakin gwamnan.

"Lamarin ya ritsa da wani direba a ayarin motoccin mataimakin gwamnan kuma direban wanda dan sanda ne ya mutu tare da wani mutum daya, mai daukan hoto a ayarin motoccin.
"Wadanda suka jikkata suna asibiti suna karbar magani a Asibitin Koyarwa ta Usmanu Dan Fodio da ke nan Sokoto.
"Lamarin ya faru ne a hanyarsu na dawowa daga Karamar Hukumar Sabon Birni zuwa Sokoto."

Kara karanta wannan

Alumundahar N37bn: Ministan gwamnatin Buhari Sadiya Farouq ta yi biris da gayyatar EFCC

Asali: Legit.ng

Online view pixel