Wani Bature Matukin Jirgin Sama Ya Garzayo Afrika Don Zabo Mata Daga Kauye, Ya Aureta
- Wani bidiyo dake yawo na wani bature da ya auri wata budurwa yar kauye a nahiyar Afrika ya girgiza intanet
- A bidiyon da ke yawo a TikTok, an gano baturen rike da dan da suka haifa yayin da yake bada labarin halin da matarsa ta shiga a lokacin haihuwa
- Jama'a sun garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu kan auren da aka kulla tsakanin masoyan biyu da suka fito daga nahiya daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani matukin jirgin sama bature ya nuna soyayya ta gaskiya yayin da ya garzayo nahiyar Afrika domin auren wata budurwa yar kauye a kasar Kenya.
A wani bidiyo da @hajabangura965 ya wallafa a TikTok, an gano baturen zaune a kusa da sahibar tasa rike da yaronsu a hannu.
Bature mai tukin jirgin sama ya auri bakar fata
Matashiyar yar Kenyan wanda wasu suka yi ikirarin cewa tana da kunya ta bar mutane suna tambayar yadda aka yi ta ja hankalinsa har ya fada tarkon sonta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dauki tsantsar son da baturen ke yi mata a bidiyon inda ya bayar da labarin halin da matar tasa ta shiga a lokacin haihuwa.
Tunawa da ya yi da bayanin halin da matar ta shiga ya nuna irin so da kulawar da yake mata.
Jama'a sun yi martani bayan bature ya auri bakar fata
Mutane da dama sun cika da zumudin son sanin yadda matukin jirgin saman ya fada tarkon sonta. Wasu sun yi ikirarin ta yi masa asiri ne.
@quinterakinyi912 ta ce:
"Yanzu na yarda cewa so makaho ne."
Houseof Chimee ta ce:
"Hmmm! me yasa nake cin wani al'amari."
Nadula nghelo_na ta yi martanu:
"Ya taki sa'ar samunta. Tana da kyau!"
@user88190582075314 ta yi martani:
"A ina kika hadu da shi don muma mu fara yawo ta wurin wa ya sani ko zan taki sa'a."
Mama ka spunky ta ce:
"Duk zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ha maza ha mata sai ya yi."
Highstreetfinds ta ce:
"Wai matukin jirgin sama kuke nufi!!!"
Kalli bidiyon a kasa:
Matar aure ta fadi makudan kudaden da take samu
A wani labarin kuma, wata matar aure da ke zaune a kasar Dubai ta girgiza intanet bayan ta bayyana cewa attajirin mijinta na bata KSh miliyan 37 duk wata a matsayin alawus.
A cikin wani bidiyo da ya dauka hankali a Instagram, Malaikah Raja ta bayyana yadda take kashe makudan kudade daga asusun mijinta, Mohammed Fuaadh.
Asali: Legit.ng