Kotu Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Kasafin Kudi da 'Yan Majalisun Jihar PDP Suka Amince, Akwai Aiki
- Yayin da rikicin siyasa ke munana a Rivers, kotu ta yanke hukunci kan sahihancin kasafin kudin jihar
- Kotun da ke zamanta a Abuja ta dakatar da amincewa da Majalisar jihar Rivers ta yi na kasafin kudin shekarar 2024
- Hakan ya biyo bayan rattaba hannu da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi bayan amincewa da kasafin kudin da Majalisar ta yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da amincewa da Majalisar jihar Rivers ta yi kasafin kudin shekarar 2024.
Mai Shari'a, James na kotun Tarayyar ya soke amincewa da kasafin har na naira biliyan 800 da suka amince da shi, cewar Leadership.
Wane hukunci kotun ta yanke a Rivers?
Bayan amincewar Majalisar karkashin jagorancin Edison Ehie, Gwamna Siminalayi Fubara ya rarraba hannu kan kasafin kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun har ila yau, ta amince da korafin kakakin Majalisar, Martin Amaewhule a kotun kan matakan Gwamna Siminalayi Fubara.
Martin na neman kotun ta dakatar da gwamnan daga cin zarafi da kuma katsalandan a lamarin Majalisar karkashin jagorancinsa da sauran matsaloli.
Yadda rikicin Rivers ya fara
A ranar 13 ga watan Disamba, gwamnan ya gabatar da kasafin kudin a gaban 'yan Majalisu guda biyar kacal karkashin jagorancin Edison Ehie.
Hakan ya biyo bayan rushe Majalisar da gwamnan ya yi inda ya gabatar da kasafin kudin a cikin gidan gwamnatin jihar.
Sauran 'yan Majalisun sun sauya sheka ne zuwa jam'iyyar APC daga PDP yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a jihar.
Channels TV ta tattaro cewa wadanda suka sauya shekar zuwa APC na goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.
An rushe Majalisar jihar Rivers
A wani labarin, Gwamna Siminalayi Fubara ya ba da umarnin rushe Majalisar jihar Rivers da ke birnin Port Harcourt saboda wasu dalilai
Gwamnan daga bisani ya bayyana dalilin rushe Majalisar inda ya ce za a yi mata kwaskwarima ne.
Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasa ke kara kamari tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng