Yayin da Aka Watse Aka Bar Shi, Gwamnan PDP Ya Gabatar da Kasafin 2024 Gaban 'Yan Majalisu 5 Kacal
- Gwamnan jihar Rivers ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 a gaban mambobin Majalisar jihar biyar kacal
- Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin ne a gidan gwamnatin jihar bayan fara rushe Majalisar da safiyar yau
- Wannan na zuwa ne yayin da ke ci gaba da rikici tsakanin gwamnan da mai gidansa, Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 a gaban mambobin Majalisar jihar.
Sai dai abin mamaki gwamnan ya gabatar da kasafin ne a gaban mambobin Majalisar guda biyar kacal wadanda ke tsaginsa, Legit ta tattaro.
Wane mataki Majalisar ta dauka kan mambobin?
Wannan na zuwa ne bayan 'yan Majalisun jihar 27 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani kakakin Majalisar ya yi zama da mambobin tsagin gwamnan guda biyar inda ya ayyana rusa zaben sauran 'yan Majalisar.
Gwamnan ya gabatar da kasafin a wani kebabben wuri a gidan gwamnatin jihar bayan fara rushe Majalisar da safiyar yau.
Siminalayi ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 har naira miliyan 800 a gaban Majalisar a yau Laraba 13 ga watan Disamba.
Wane hukunci kotun ta yanke kan kakakin Majalisar?
Ana zargin 'yan Majalisar da su ka sauya shekan na goyon bayan Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
Har ila yau, kotu ta yi hukunci kan sahihancin shugabancin kakakin Majalisar jihar, Edison Ehie.
Kotun ta tabbatar da Ehie a matsayin halastaccen kakakin Majalisar jihar da aka tumbuke a kwanakin baya.
Kotun ta gargadi sauran mambobin Majalisar da ke tsagin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike kan shiga zaman Majalisar a nan gaba inda ta gindaya sharuda.
An rushe Majalisar jihar Rivers
A wani labarin, da safiyar yau ce Laraba aka wayi gari inda aka fara rushe Majalisar jihar Rivers.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike.
Daga bisani mambobin sun yi zama a gidan gwamnatin jihar inda su ka rusa zaben mambobin Majalisar da su ka koma APC.
Asali: Legit.ng