Jirgin Rano Air Zai Fara Jigilar Fasinja a Jihohin Katsina da Kaduna, an Ga Sakamako
- Rano Air ya sanar da fara jigilar fasinja a jihohin Kaduna da Katsina shekara guda bayan fara aiki a Najeriya
- Fasinjoji na cigaba da karbar ayyukan jirgin da aka bayyana yana da saukin farasi sabanin sauran jirage
- Najeriya na da kamfanonin jirage da yawa, amma tsada kan hana jama’a yin tafiya ta wannan hanya mafi sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - A ranar 21 ga watan Janairun 2024 ne jirgin saman Rano Air zai fara jigilar fasinja daga jihar Katsina zuwa Abuja da kuma Kaduna zuwa Legas.
Rano dai na daga cikin kamfanonin jiragen saman da suka fara jigila a shekarar da ta gabata, wanda ke jigila daga Abuja zuwa Legas, Kano, Sokoto da birnin Maiduguri.
Rahotanni sun bayyana cewa, fasinjoji da yawa sun bayyana, inda suka nuna jin dadi da samun damar tashin jirgin zuwa jihohinsu.
Yadda fasinjoji suka karbi jirgin
A cewar majiya, an samu fasinjoji ainun daga jihohin Katsina da Kaduna a yau, inda da yawa ke bayyana jin dadinsu na ganin karshen dogon jira da dawainiyar sufuri a jihohin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin Rano Air dai na cigaba da samun karbuwa, inda jama’a ke haba-haban shiga jirgin mai daukar mutane 50 a zubi guda, Daily Trust ta ruwaito.
Daga shekarar da ta gaba zuwa yanzu, fasinjoji kan kara karbar jirgin, inda suke samun saukin jigila da araha sabanin sauran jirage.
Shirin Rano Air a nan gaba
Bayan kaddamar da jigila a jihohin Katsina da Kaduna, Rano Air ya bayyana kwarin gwiwar fadada ayyukansa a sauran jihohin Najeriya.
Akwai jirage da yawa da ke zirga-zirgar fasinja a cikin gida Najeriya, sai dai tsada kan hana mutane da yawa hawa jiragen.
Man jirgi ya yi tsada a Najeriya
A wani labarin, kungiyar masu jiragen sama ta Najeriya (AON) a ta taba sanar da dakatar da harkokinta daga ranar Litinin, 9 ga watan Mayun 2022 saboda tsadar man jirgi wanda ya kai N700 kan kowace lita.
Kungiyar ta koka da cewa Jet A1 ya kashe kudin gudanar da ayyuka zuwa sama da kashi 95 cikin dari, wanda hakan ya janyo wa fasinjoji wahala, rahoton Daily Trust.
Shugaban kungiyar Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ne ya bayyana hakan a cikin wata wasika zuwa ga ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika, wanda aka kuma aika kwafinta zuwa ga babban daraktan NCAA.
Asali: Legit.ng