Tsadar rayuwa: Ba a gama jimamin matsalar man mota ba, man jirgi ya sa jirage za su daina tashi a Najeriya

Tsadar rayuwa: Ba a gama jimamin matsalar man mota ba, man jirgi ya sa jirage za su daina tashi a Najeriya

  • Kungiyar masu jiragen sama ta Najeriya (AON) ta sanar da shirin rufe ayyukanta a fadin kasar nan
  • AON ta ce dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa, saboda karin farashin man jiragen sama da ya kai N700 kan kowace lita
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kungiyar, Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya aikewa ministan sufurin jiragen sama

Kungiyar masu jiragen sama ta Najeriya (AON) ta sanar da dakatar da harkokinta daga ranar Litinin, 9 ga watan Mayu saboda tsadar man jirgi wanda ya kai N700 kan kowace lita.

Kungiyar ta koka da cewa Jet A1 ya kashe kudin gudanar da ayyuka zuwa sama da kashi 95 cikin dari, wanda hakan ya janyo wa fasinjoji wahala, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Tsadar rayuwa: Ba a gama jimamin matsalar man mota ba, man jirgi ya sa jirage za su daina tashi a Najeriya
Tsadar rayuwa: Ba a gama jimamin matsalar man mota ba, man jirgi ya sa jirage za su daina tashi a Najeriya Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Shugaban kungiyar Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ne ya bayyana hakan a cikin wata wasika zuwa ga ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika, wanda aka kuma aika kwafinta zuwa ga babban daraktan hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) rahoton Daily Post.

Hakazalika sanarwar ta samu goyon bayan manyan shugabannin kamfanonin jiragen sama na gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yayin da AON ke yabawa da kokarin gwamnati mai ci karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari don tabbatar da bunkasa sufurin sama a Najeriya, abun bakin ciki, farashin man jirgi na ci gaba da hauhawa lamarin da ya haifar da matsin lamba ga dorewar ayyuka da kuma kudin jiragen. Wannan ba mai dorewa bane kuma kamfanonin jiragen saman ba za su iya daukar matsin lamban ba.
“Saboda haka, kungiyar masu jiragen sama ta Najeriya (AON) na danasanin sanar da jama’a cewa kamfanonin jiragen za su dakatar da harkoki a fadin kasar daga ranar Litinin, 9 ga watan Mayun 2022 har sai baba-ta-gani.

Kara karanta wannan

An kuma, Bam ya tashi a kusa da sansanin Sojojin Najeriya a babban birnin jihar Arewa

“AON na amfani da wannan kafar don bayyana cewa mun yi nadamar duk wani cikas da wannan hukuncin zai iya haddasawa sannan muna rokon matafiya da su sake la’akari da tsarin tafiyarsu sannan su nemi mafita."

Dole kasashen Afrika su shiryawa muguwar yunwar da za a fuskanta - Shugaban bankin AfDB

A wani labarin, Shugaban babban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fitar da jawabi yana cewa dole Afrika ta shiryawa matsalar kayan abinci da za a fuskanta.

Dr. Akinwumi Adesina ya ce yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine zai jawo yunwa a Duniya. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu 2022, an ji cewa Dr. Adesina ya yi magana a game da Afrika a wajen wani taro da aka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel