Adesina Ya Tuna da Yadda Buhari Ke Ambatan Sunan Yesu a Sadda Yake Mulki
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ambaci sunan Yesu
- Adesina ya ce Buhari ya ambaci sunan 'Yesu' lokacin da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama
- Ya ce tsohon shugaban kasar ba mai zafafawa a addini bane kamar yadda aka sanar da yawancin yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ambaci sunan 'Yesu' lokacin da jirgin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kusa kifewa a watan Fabrairun 2019.
Adesina ya bayyana hakan ne a cikin littafin da ya rubuta kan tsohon shugaban kasa Buhari.
Buhari ya faɗi dalilin da ya sa gwamnatinsa ba ta kashe wani shugaban ƴan ta'adda ba, ta yi masa gata 1
A cewar Jaridar Daily Trust, Adesina ya ce Buhari ba mai zafafawa a addini bane kamar yadda mutane da dama ke yi masa kallo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mataimakin shugaban kasar ya tsira daga hatsarin jirgin sama a 2019. Shugaban kasar ya taya shi murna a bainar jama'a, sannan ya sake taya mataimakin shugaban kasar murna a taron majalisar zartarwa da aka yi a gaba.
"Cike da barkwanci ya ce: 'Har na hango lokacin da jirgin ya fado da kara, na san mataimakin shugaban kasa a matsayinsa na fasto ya yi ihun, Yesu! Yesu! Yesu! Kuma abun farin ciki, Yesu bai yi nisa da shi ba, don haka ya cece shi'.
"Sai muka yi dariya gaba daya. Amma babban darasi daya. Masu zafafawa basa son Yesu. Basa taba son jin sunansa, ko alakanta wani abun al'ajabi gare shi."
Yadda jirgin Buhari ya kusa kifewa
A wani labarin, mun ji cewa jirgin da ya dauko Muhammadu Buhari ya kusa yin hadari dauke da mukarrabansa lokacin da yake karagar mulki.
Vanguard ta kawo rahoton wannan abin da ya faru a Nuwamban shekarar 2015 kamar yadda ya zo a littafin tarihin shugaban.
Kamar yadda Femi Adesina ya rubuta a littafin na sa, jirgin ya dauko Muhammadu Buhari ne da nufin halartar taro a tsibirin Malta.
An shirya Mai girma shugaban Najeriya na lokacin zai yi zama da sauran kasashen renon Birtaniya, sai aka samu matsala a hanya.
Asali: Legit.ng