Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Lakume Gidaje 50 a Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Lakume Gidaje 50 a Jihar Arewa

  • An tafka asara a jihar Benue bayan wata mummunar gobara ta tashi a wani ƙauye na ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma
  • Gobarar wacce ta tashi lokacin da mutanen ƙauyen ke tsaka da gudanar da ayyuka a gonakinsu, ta ƙone gidaje 50
  • Cikin mutanen da gobarar ta ritsa da su har da wata tsohuwa mai shekara 80 a duniya wacce ta rasa ranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50 a ƙauyen Tse-Agubor Gyaruwa da ke gundumar Tsambee-Mbesev a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benue.

Shugaban ƙauyen da abin ya shafa, Cif Ayatse Agubor, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, yayin da mutanen ƙauyen ke aiki a gonakinsu, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana cikin matsalar rashin tsaro, ministan tsaro ya fadi abu 1 da ya kamata yan Najeriya su yi

Gobara ta lakume gidaje 50 a Benue
Mummunar gobara ta lakume gidaje a Benue Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Ya ce mahaifiyarsa ƴar 80 da gobarar ta kashe ba ta samu wanda zai taimaka mata daga gadon jinya ba saboda mutane ba sa gida a lokacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tafka mummunar asara

Agubor ya danganta gobarar da ƙona daji ba tare da izini ba, yana mai gargaɗin matasan ƙauyen da su guji aikata hakan ko kuma su fuskanci fushin hukuma, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen, Hajiya Kongo, wacce ta yi asarar sama da buhu 10 na masara, wake, waken suya, tufafi da sauran kayayyakin gida ciki har da N110,000 da ta boye a cikin buhunan masarar da ta ƙone, ta koka kan irin ɓarnar da gobarar ta yi a gidanta.

Ta roƙi ɗaiɗaikun mutane da gwamnati da su kawo mata ɗauki.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwer West, Henry Agba, yayin da yake mayar da martani kan lamarin, ya ce majalisar ƙaramar hukumar ba za ta ƙara amincewa da ƙona daji ba a yankin.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a dakin taro na Ahmed Musa, bayanai sun fito

Agba ya ƙara da cewa za a kafa wata tawaga da za ta tantance girman ɓarnar da gobarar ta yi domin ba majalisar damar kai rahoto ga hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha (SEMA).

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ba ta amsa kira ko dawo da amsar saƙonnin da aka aika ta wayar tarho kan lamarin ba.

Gobara Ta Laƙume Kasuwa a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tafka asara bayan wata mummunar gobara ta tashi a wata kasuwa a jihar Rivers.

Gobarar ta tashi ne a kasuwar katako ta Oyigbo da ke jihar, inda ta lalata kayan miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng