Dakarun Sojin Sama Sun Sheke Kasurgumin Shugaban Yan Ta'adda, Bayanai Sun Fito

Dakarun Sojin Sama Sun Sheke Kasurgumin Shugaban Yan Ta'adda, Bayanai Sun Fito

  • Dakarun sojojin sama sun samu gagarumar nasarar kawar da wani ƙasurgumin shugaban ƴan ta'adda a Kaduna
  • Sojojin na Operation Whirl Punch sun halaka ƙasurgumin ɗan ta'adda Janari tare da wasu daga cikin mayaƙansa
  • Janari da mayaƙan nasa sun gamu da ajalinsu ne bayan an hango suna shirin kai hari kan bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun rundunar sojin sama na Operation Whirl Punch sun samu nasarar halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan ta'adda, wanda aka fi sani da Janari da wasu mayaƙansa.

Sojojin sun halaka Janari ne a hare-haren da suka kai ta sama a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairun 2024, cewar rahoton Daily Trust.

Sojin sama sun sheke kasurgumin dan ta'adda
Sojojin sama sun halaka shugaban yan ta'adda a Kaduna Hoto: Nigerian Airforce
Asali: Facebook

Wannan dai na ƙunshe ne a cikin sanarwar da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Lahadi, 21 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Ana cikin matsalar rashin tsaro, ministan tsaro ya fadi abu 1 da ya kamata yan Najeriya su yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janari da tawagarsa dai na da alhakin kai hare-hare da sace-sacen mutane a jihar Kaduna da ma kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Yadda aka kai harin

Gabkwet ya ce an amince da kai harin ne bayan da aka ga Janari da ƴan ƙungiyarsa a wani wuri kusa da Gadar Katako a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa suna yin taro ne don yiwuwar kai hari ko kuma sace fararen hula, wanda hakan ya sanya aka farmake su.

Bayanan sirri da aka samu bayan harin sun nuna cewa lallai an kawar da Janari tare da wasu ƴan ta’adda/masu garkuwa da mutane da dama.

Ya kuma ƙara da cewa an kai makamancin irin wannan harin ta sama a ranar 20 ga watan Janairun 2024 kan maboyar ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kusa da Chukuba a Jihar Neja tare da samun nasarori daban-daban.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke manyan kwamandojin yan ta'adda, sun ceto mutum 27

Legit Hausa ta samu jin ta bakin Salis Tukur wanda ya nuna jin daɗinsa kan wannan nasara da sojojin suka samu.

Salis ya bayyana cewa kisan Janari abun a yaba ne domin ya daɗe yana aikata ayyukan ta'addanci kan bayin Allah.

Ya yaba wa sojojin kan wannan nasarar da suka samu inda ya yi addu'ar Allah ya kare su ya kuma ƙara musu ƙarfin gwiwar cigaba da kakkaɓe ƴan ta'adda.

Sojoji Sun Ragargaji Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun ragargaji ƴan bindiga a wani samame da suka kai a jihar Benue.

Sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutum 27 da ƴan bindigan suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng