Yan Sanda Sun Kama Mutumin da Ya Kitsa Garkuwa da Kansa Don Damfarar Yan uwansa a Abuja
- Wani matashi ya taki rashin sa'a a kokarinsa na damfarar yan uwansa duk da cewar ya kitsa garkuwa da kansa
- Rundunar yan sandan babban birnin tarayya ta kama mutumin kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ta saki a ranar Asabar, 20 ga watan Janairu
- SP Josephine Adeh, kakakin yan sandan ta kuma bayyana cewa rahotannin garkuwa da mutane a rukunin gidajen River Park ba gaskiya bane
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Hukumomin yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun yi watsi da rahotannin da ke yawo game da batun garkuwa da mutane da ya afku a rukunin gidaje na River Park a safiyar Asabar, 20 ga watan Janairu.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar yan sandan FCT ta bayyana rahotannin a matsayin kanzon kurege sannan ta nanata cewa babu wanda aka sace a rukunin gidajen River Park.
Sanarwar dauke da sa hannun SP Josephine Adeh, kakakin rundunar yan sandar, ta kuma nuna cewa wani matashi mai suna Nnandi Agu na Games Village ya shiga hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rundunar, an kama Agu ne bayan ya kitsa garkuwa da kansa domin damfarar dan uwansa da yake zaune a rukunin gidajen.
Sanarwar ta ce:
"Rundunar yan sandan FCT na sane da labaran da ke yawo game da zargin garkuwa da mutane a rukunin gidajen River Park a safiyar yau sannan tana fatan bayyana cewa sabanin rahotannin, babu wanda aka sace a rukunin gidajen River Park.
"Kawai dai wani Nnandi Agu na unguwar Games Village ne ya kitsa garkuwa da kansa a kokarin damfarar dan uwansa da ke zaune a rukunin gidajen.
"Yanzu haka wanda ake zargin yana tsare a hannun yan sanda ana yi masa tambayoyi.
"Yayin da ake ci gaba da bincike, a a sanar da jama'a halin da ake ciki."
Yan uwan Nabeeha sun shaki iskar yanci
A wani labarin kuma, mun ji cewa ragowar ‘yanuwan Nabeeha Al-Kadriyah da aka yi garkuwa da su, sun samu ‘yanci kamar yadda muka samu labari.
Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa miyagun ‘yan bindiga sun fito da sauran ‘yanuwan marigayiyar da aka hallaka.
Asali: Legit.ng