An Tafka Asarar Miliyoyin Naira Bayan Gobara Ta Tashi a Wata Fitacciyar Kasuwa

An Tafka Asarar Miliyoyin Naira Bayan Gobara Ta Tashi a Wata Fitacciyar Kasuwa

  • An tafka asarar kayayyakin miliyoyin naira bayan wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Oyigbo da ke jihar Rivers
  • Gobarar dai ta tashi ne a babbar kasuwar katako ta Oyigbo inda ta laƙume kayayaki na miliyoyin naira
  • An bayyana cewa gobarar wacce ta tashi cikin dare ta auku ne a sanadiyyar wani haɗi ba bisa ƙa'ida ba da aka yi na wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Kayayyakin da suka haɗa da injinan yankan katako da na’urorin samar da wutar lantarki da kuɗinsu ya kai miliyoyin naira sun lalace a wata gobara da ta tashi da tsakar dare a jihar Rivers.

Gobarar dai ta tashi ne a babbar kasuwar katako ta Oyigbo da ke laramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An yi wa shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, fashi a Landan

Gobara ta tashi a jihar Rivers
Gobara ta lakume kayayyaki a wata kasuwa ta jihar Rivers Hoto: FedFireNG
Asali: Facebook

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na daren ranar Alhamis, biyo bayan kama wa da wuta da wani haɗi na wutar lantarki da aka yi ba bisa ƙa'ida ba a kasuwar, bayan an dawo da wutar lantarki, rahoton The Punch ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa wacce ta bayyana sunanta da Chioma ta koka da cewa:

"Lokacin da suka dawo da wutar lantarki ne, saboda ina zaune kusa da kasuwar, na ji wata ƙara mai ƙarfi kuma abu na gaba shi ne sai wuta ta kama, kuma tana yaɗuwa cikin sauri.
"An lalata injina da yawa, injinan yankan katako da janaretoci. Babu ɗaya daga cikin injinan wanda bai kai N2m ko N3m.
"Dukkansu sun lalace kuma ba a bar mu da komai ba. Wannan (kasuwancin) shine kawai abin da nake yi don biyan kuɗin makarantar yarana.

Kara karanta wannan

"Taku ta ƙare" An kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi mutanen Abuja

Me hukumomi suka ce kan gobarar?

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce za ta yi bincike sannan ta ba da cikakken bayani.

Sai dai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba ta yi hakan ba.

Gobara Ta Tashi a Kasuwar Panteka

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobara a kasuwar Panteka da ke jihar Kaduna.

Gobarar wacce ta shafi ɓangaren ƴan katako na kasuwar ta janyo an tafka asara mai yawan gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng