Wani matashi mai suna Haruna Inka Kankiya ya rasa rayuwarsa

Wani matashi mai suna Haruna Inka Kankiya ya rasa rayuwarsa

Wani matashi mai suna Haruna Inka Kankiya ya rasa rayuwarsa sanadiyyar gasar wasan ruwa da aka shirya don bikin Sallah a karamar hukumar Kankiya dake jihar Katsina

Wakilin Legit.ng ya ruwaito cewa matashin ya rasa rayuwarshi ne bayan ya lashe zagaye na farko dana biyu da aka shiryawa gasar a yayin gudanar da zagaye na ukun ne ya tarar da ajalinsa bayan ya kwashe sama da mintuna 40 a cikin ruwan hakan ne tasa alkalan wasan suka bada damar shiga don lalubo matashin wanda daga bisani aka tabbatar da ya rasu a cikin ruwan.

Wasan ya zamo irinsa na biyu kenan daya taba gudana a garin na Kankiya wanda a shekarar data gabata aka shirya makamancinsa a wannan wuri kuma aka kammala lafiya.

Gasar ta samu halartar Hakimin Kankiyan Alhaji Musa Hassan Sada da dagattai da masu unguwanni dama'yan siyasa wanda al’amarin ya faru a gabansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel