Rai Bakon Duniya: Ango Ya Mutu Ana Saura Kwana 3 Daurin Aurensa, Amarya Ta Kusa Hauka
- Ana shirin daura auren wani saurayi da masoyiyarsa, ciwon ajali ya kama shi, ya amsa kiran mahaliccinsa a gadon asibiti
- An ruwaito cewa saura kwana uku kadai ya rage a daura auren Basif da Praise, saurayin ya rasu, lamarin da ya jefa mutane cikin tashin hankali
- Ranar da ya kamata ta zamo ta farin ciki ga amaryar, ta koma ta bakin ciki da kuka, tana mai cewa ba za ta taba samun madadin Basif ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kogi - Wani matashi da ake shirin daurin aurensa a ranar 23 ga watan Disamba, ya koma ga mahaliccinsa a ranar 20 ga wata, ana saura kwana uku a daura auren.
Wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Omala da ke jihar Kogi, inda matashin mai suna Abraham Basif ke shirin auren masoyiyarsa Praise Enyojo, sai kuma ajali ya riske shi.
Matashin ya kwanta rashin lafiya
Har an gama dukkanin shirye-shirye na baikon masoyan a gidan wani dattijo Ahmodu Jonah, yayin da za a daura auren a coci washe gari, amma farin ciki ya koma bakin ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tsaka da shirye-shiryen bikin ne matashin ya kwanta rashin lafiya, aka garzaya da shi asibiti. Kowa na tunanin za a sallami Basif kafin ranar daurin auren shi.
Sai dai Basif ya ce "ga garinku nan" ana saura kwana uku daurin auren, lamarin da ya jefa kowa a garin cikin bakin ciki da jimamin wannan mutuwar.
Halin da amaryar ta shiga
Mutuwar Basif a cewar jaridar The Nation ta ruguza duk wani buri na masoyiyarsa Praise, wacce ta kwallafa rai akan zama tare da shi har karshen rayuwarta, mutuwarsa ta girgiza ta.
Praise ta kasance cikin bakin ciki da kuka tun bayan sanar da mutuwar Basif, duk wani yunkuri na iyalanta su rarrasheta ya ci tura.
An ruwaito cewa Praise ta hadu da Basif ne a garin Lokoja ta dalilin wata aminiyarta, inda suka fara yin kawance, daga bisani suka yanke shawarar auren juna.
Tallafin COVID-19: Gwamnatin Jigawa ta dakatar da jami'ai 28
A wani labarin, gwamnatin jihar Jigawa ta dakatar da shugaban shirin Fadama III tare da manyan jami'ai 27 daga aiki
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an sun karkatar da kusan naira biliyan 1.7 a shekarar 2022 bayan da aka basu aikin raba Tallafin COVID-19 ga marasa galihu a jihar
Asali: Legit.ng