Idan kun shirya aure, ku guji mata yan kasa da shekara 25 – Wani sabon ango ya shawarci maza

Idan kun shirya aure, ku guji mata yan kasa da shekara 25 – Wani sabon ango ya shawarci maza

Wani dan Najeriya da yayi aure kwanan nan ya shawarci maza da su guji mata yan kasa da shekaru 25 idan za su nemi aure.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin zumunta, mutumin mai suna Olaseni yace shekaru 25 ne lokacin da mata suke sanin ko me suke bukata a rayuwarsu.

“Bari in kara jaddada muku cewa. Idan ka shirya yin aure, guji mata wadanda suka kasance kasa da shekaru 25 sai dai idan ka tabbatar da cewa kana iya biya musu bukatunsu don kwantar musu da hankali. Kada kayi wa kanka karya”.

A yayinda yake bayyana yanda aka yi yazo da wannan irin ra’ayin, ya bayyana cewa mata yan kasa da shekaru 25 su kan kasance cikin shirin aure cikin shekaru biyu.

Idan kun shirya aure, ku guji mata yan kasa da shekara 25 – Wani sabon ango ya shawarci maza
Idan kun shirya aure, ku guji mata yan kasa da shekara 25 – Wani sabon ango ya shawarci maza
Asali: Instagram

“LMAO. Wannan tamkar abunda na fuskanta ne da kuma wassu yan kalilan; wannan lokacin ya kasance lokacin jan hankali ga yawanci kuma zasu bayyana zuciyarsu a ko ina a shekaru biyu.”

KU KARANTA KUMA: Nagode da baka musuluntar dani ba – Rotimi Amaechi ga Shugaba Buhari

Rubutunsa na nuni ga cewa mata yan kasa da shekaru 25 su kan kasance basu da ra’ayin shiga zamantakewa na gaskiya sai wasa.

A wani lamari na daban, mun ji yadda wasu iyaye suka yanke shawarar aurar da kananan yaransu mata domin samun kayan abinci a sansanin yan gudun hijira da ke Daudu, karamar hukumar Guma na jihar Benue.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yunwa da cututtuka, musamman cutar gudawa suka bazu a sansanin. Tuni dai an tabbatar da mutuwar mutane takwas sakamakon cutar yunwa da sauran cututtuka a sansanin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng