Ana saura makonni uku aurensa ya rasu

Ana saura makonni uku aurensa ya rasu

Babu iyayen da zasu ji dadi su rasa yayansu. Addu'an da suke kulli yaumin shine kowanne daga cikin yaransu su rayu, suyi aure kuma su haifa musu jikoki.

Irin wannan abu ya faru a rahoton da muka samu inda wani matashin Najeriya mai suna Adejoh Noah wanda ya mutu ana saura makonni uku daurin aurensa. Wannan abin takaicin ya faru ne bayan ya rabawa jama'a katin aurensa.

A katin da ya raba, za'a daura masa aure da masoyiyarsa Jemila Mohammed, ranan 28 ga watan Disamba, 2018 a garin Ankpa, jihar Kogi.

Ana saura makonni uku aurena ya rasu

Ana saura makonni uku aurena ya rasu
Source: UGC

Wasu daga cikin abokansa sun mika sakon ta'aziyyarsu a shafin sada ra'ayi da zumuntar Facebook. Daya daga cikinsy Akor Martins yace: "Na karbi sakon gayyata zuwa daurin aurensa ranan Talata amma na samu sakon rasuwarsa a Yau. Allah ya jikansa."

Ana saura makonni uku aurena ya rasu

Ana saura makonni uku aurena ya rasu
Source: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel