Wata Mata ta mutu wajen gasar cin kayan kwalama a Kasar waje

Wata Mata ta mutu wajen gasar cin kayan kwalama a Kasar waje

Wata mata ta mutu yayinda ta shiga gasar cin kayan kwalama don raya ranar kasar Australia, gidan jaridar kasar ta ruwaito a ranar Litinin.

Rahoton ya nuna cewa an kira masu bayar da agajin gaggawa a Jihar Queensland a ranar Lahadi bayan da matar ta shiga cikin wani mawuyacin hali.

An tattaro cewa matar mai shekara 60 ta samu daukewar numfashi bayan ta cunkusa kayan makulashen a cikin bakinta.

Cincin din mai suna Lamingtons ya kasance kayan makulashe na gargajiya da ake dilmiya shi cikin zuma da kwakwa.

An kai matar asibiti cikin gaggawa a Hervey Bay amma daga bisani sai ta mutu, kafar labarai ta ABC ta ruwaito.

A wani rubutu da hukuma da ma’aikatan otel din suka wallafa a shafin Facebook sun mika ta’aziyya ga iyalai da abokan arziki na matar.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwa yar shekara 60 ta yi aurenta na farko tare da burin ranta (hotuna)

Yan sandan kasar sun ce babu wanda ake zargi kan lamarin sannan kuma za a shirya rahoto don bikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel