Tallafin COVID-19: Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar da Jami’an da Aka Kama da Laifin Karkatar da N1.7bn
- Gwamnatin jihar Jigawa ta dakatar da daraktan shirin Fadama III da manyan jami'an shirin su 27 saboda zargin almundahana
- Gwamnan jihar Umar Namadi ne ya ba da umurnin sallamar jami'an bayan kama su da karkatar da kudin tallafin COVID-19
- A watan Satumba ne gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin NG-J-CARE don rabon tallafin naira biliyan 1.7 ga talakawan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta dakatar da jami’an da aka dorawa alhakin raba naira biliyan 1.7 na tallafin annobar COVID-19 a jihar bisa zargin sun karkatar da kudaden.
Shirin wanda gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Duniya suka bullo da shi, an yi shi ne da nufin rage radadin illar da cutar COVID-19 ta yi ga marasa galihu a Najeriya.
Wadanda aka tsara su ci gajiyar shirin, mai suna NG-J-CARES a Jigawa sun hada da manoma, marasa galihu da kuma kananan ‘yan kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Namadi ya kafa kwamitin binciken badakalar
Sai dai Premium Times ta ruwaito cewa wasu daga cikin manoman da aka shirya ba tallafin sun shaida wa gwamnan jihar Umar Namadi cewa an tauye hakkinsu a wajen rabon tallafin.
Sun bayyana haka ne a lokacin da gwamnan ya kai ziyarar bazata zuwa yankunansu na karkara a watan Yulin da ya gabata.
Hakan ne ya sa gwamnan ya kafa kwamitin da zai binciki badakalar da ake zargin an tafka wajen rabon tallafin da aka gudanar a watan Satumban 2022.
Kwamitin ya gano badakala a rabon tallafin COVID-19
Kwamitin binciken da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Mustapha Makama ya jagoranta ya mika rahotonsa a ranar Talata.
Kwamitin ya tuhumi jami’an ofishin Fadama III na jihar da suka yi rabon tallafin da aikata zamba.
Kwamitin ya yi zargin cewa jami’an sun bai wa kowane manomi Naira 8,000 kacal, maimakon Naira 150,000 da kayan aikin noma da aka saka su ba su.
Gwamnatin jihar ta dakatar da jami'an shirin Fadama III
Kakakin gwamnatin jihar, Sagir Musa, a ranar Alhamis, ya ce gwamnati ta dakatar da kodinetan shirin Fadama III na jihar, Aminu Isah, da dukkan jami’an shirin su 27.
Ya ce matakin ya biyo bayan matsayar da majalisar zartarwa ta jihar da gwamnan ya jagoranta a ranar Laraba ta cimmawa.
Dalilin dauke hedikwatar Hukumar FAAN zuwa Legas - Keyamo
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta wanke kanta kan dalilin dauke hedikwatar Hukumar FAAN daga Abuja zuwa Legas.
Ministan sufurin jiragen sama ne ya lissafa dalilan bakwai, a yayin da wasu 'yan Najeriya ke zargin akwai bangaranci a matakin.
Asali: Legit.ng