Kano: Ana Rade-radin Tube Shi a Sarauta, Ado Bayero Zai Kaddamar da Gagarumin Aiki Don Talaka
- Ana cikin cece-kuce kan matsayin kujerar Sarkin Kano, Ado Bayero zai kaddamar da wani gagarumin aiki a jihar
- Sarkin zai kaddamar da asibitin kungiyar Musulunci ta Ahmadiyya Muslim Jama’at a birnin Kano
- Kaddamar da sabon asibitin zai gudana ne a gobe Asabar 20 ga watan Janairu wanda zai iya daukar marasa lafiya 100 a rana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero zai kaddamar da sabon asibitin Ahmadiyya Muslim Jama’at a birnin Kano.
Kaddamar da sabon asibitin zai gudana ne a gobe Asabar 20 ga watan Janairu wanda zai iya daukar marasa lafiya 100 a rana, cewar Tribune.
Mene Sarkin Kano, Ado Bayero zai kaddamar a Kano?
Asibitin da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri har ila yau, Sarkin ne ya kaddamar da kafa tubalin gina asibitin a watan Yulin shekarar 2021.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda kungiyar Musuluncin ta ce a cikin wata sanarwa, Sarkin zai samu rakiyar sarakuna da ke yankinsa, World Top News ta tattaro.
Sauran wadanda ake sa ran za su halarci taron sun hada da masu mukamai a gwamnatin jihar da Tarayya da FRSC da kuma hukumar NDLEA.
Kiraye-kirayen da ake yi a Kano kan tube Sarkin Kano
Kungiyar Musulunci ta Ahmadiyya Muslim Jama’at ta gina asibitinta na farko a shekarar 1950 a Apapa da ke Legas da kuma Kano a shekarar 1962.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ta cece-kuce kan ruguza masarautun Kano da tsohon gwamnan jihar, Abdulllahi Ganduje ya kirkiro.
Kiraye-kirayen mayar da tsohon Sarki, Sunusi Lamido sun fara tasiri wanda idan hakan ta tabbata zai maye gurbin Sarki Aminu Ado Bayero.
Da alamu Sunusi Lamido zai koma kujerarsa
A wani labarin, ana ta kiraye-kirayen mayar da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi kan kujerarsa.
Kiraye-kirayen sun fara tasiri a jihar tun bayan cin zaben Gwamna Abba Kabir a matsayin gwamnan jihar a watan Maris.
Wannan ya biyo bayan tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir a matsayin halastaccen gwamnan jihar a Kotun Koli.
Asali: Legit.ng