Abu Ya Girma: Gwamnan PDP Ya Tsige Manyan Sarakuna 1 Daga Kan Karagar Mulki Kan Abu 1
- Gwamna Adeleke ya sauke manyan sarakuna uku daga kan karagar mulki bayan kammala binciken naɗinsu a jihar Osun
- Ademola Adeleke ya fara ɗaukar mataki kan naɗe-naɗen sarakunan da magabacinsa ya yi tun a ranar da ya karɓi mulki
- Ya kuma ba da umarnin a fara shirye-shirye da bin matakan doka wajen naɗa sabbin sarakuna a masarautun 3
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya tunɓuke rawanin wasu manyan sarakuna uku a yau Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024.
The Nation ta tattaro cewa yayin rantsar da shi a ranar 28 ga Nuwamba, 2022, Gwamna Adeleke na PDP ya bayar da umarnin dakatar da sarakuna kusan 30 nan take.
A lokacin, Gwamnan ya kafa hujjar cewa an naɗa sarakunan bisa kuskure da ƙeta a daidai lokacin da gwamnatin tsohon Gwamna Oyetola ta zo gargara, Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adeleke ya kuma kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Bunmi Jenyo domin ya binciki al’amuran da suka shafi nade-naɗen da Oyetola ya yi, musamman nadin Owa na Igbajo, Are na Iree da Akirun na Ikirun.
Sarakuna uku da gwamnan ya tuge wa rawani
Watanni 14 bayan haka, Gwamna Adeleke ya fitar da sanarwan korar waɗannan sarakuna da suka haɗa da, Owa na Igbajo, Oba Adegboyega Famodun, Are na Iree, Oba Ademola Ponle da Akirun na Ikirun, Oba Yinusa Akadiri.
Matakin na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Osun, Kolapo Alimi, ya fitar ranar Alhamis a Osogbo, babban birnin jihar.
Sanarwan ta ce:
"Dangane da rahoto kan harkokin naɗin sarauta wanda Honorabul Bunmi Jenyo ya jagoranta, mun bada fifiko ga bin ka'idodin doka a matsayin tushen yanke hukunci na ƙarshe.
"A rahoton, duk matakan da aka dauka a baya dangane da nada Aree na Iree da Owa na Igbajo an soke su. Kuma ya kamata a fara aiwatar da tsarin zaɓen sabbin sarakunan Iree da Owa na Igbajo nan take.
"Game da kujerar Owa na Igbajo, takardar ta rushe tsarin zaɓen da aka yi a baya, wanda ya samar da Prince Gboyega Famodun tare da ba da umarnin zaɓo wanda ya dace a naɗa."
Kotu Koli zata raba gardama a karar jihohi 5
A wani rahoton na daban Kotun ƙoli ta zaɓi ranar da zata yanke hukunci kan kararrakin da aka kalubalanci nasarar gwamnonin jihohi biyar.
A wata takarda da ta fita yau Alhamis, kotun zata sanar da hukunci kan shari'oin jihohin gobe Jumu'a, 19 ga watan Janairu, 2024.
Asali: Legit.ng