Gwamna Adeleke Ya Tube WA Sarakuna 3 Rawaninsu a Jiharsa, Ya Bayyana Dalili

Gwamna Adeleke Ya Tube WA Sarakuna 3 Rawaninsu a Jiharsa, Ya Bayyana Dalili

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tube rawanin wasu sarakunan gargajiya uku ta hanyar fitar da takardar sanarwa.

Sarakunan da abin ya shafa sun hada da Oba Adegboyega Famodun, Owa na Igbajo, Oba Ademola Ponle, Are na Iree, da Oba Yinusa Akadiri, Akirun na Ikirun.

Adeleke ya tsige rawanin sarakuna uku a jiharsa
Gwamna Adeleke ya bada umurnin zaben sarakuna uku. Hoto: Photo Credit: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fitar da wannan sanarwan ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, Kolapo Alimi, wanda ya ce gwamnan ya rattaba hannu kan takardar shawarwari da Majalisar Kolin Jihar ta amince da ita.

An dauki wannan matakin ne bayan sahihin bincike da wata kwamiti ta musamman karkashin jagorancin Gwamna Adeleke ta yi, don nuna adalcinsa da bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamnan PDP ya tsige manyan sarakuna 3 daga kan karagar mulki kan abu 1

Sanarwar ta ce:

"Bisa rahoton takardar gwamnati, an soke dukkan matakai da aka dauka na nada Aree na Irre da Owa na Igbajo.
"Kuma za a fara shirin zaben sabon Aree na Iree da Owa na Igbajo nan take. Musamman kan masarautar Aree na Iree, ana kira ga hakimai su janye karar da suka kai kotu don bada damar zaben sabon sarki bisa tsarin al'ada.
"Dangane da kujerar Owa na Igbajo, takardar gwamnatin ta soke zaben da aka yi a baya wacce ta samar da Yarima Gboyega Famodun kuma ta umurci a fara shirin zaben sabon Owa. A kan kujerar Akirun, takardar ta umurci dukkan bangarorin su jira hukunin Kotun Daukaka Kara. Yanzu ba bu kowa kan kujerar."

Alimi ya ce an umurci hukumomi su kafa kwamiti wacce za ta karbo dukkan motoccin da aka bai wa gwamnatin Gboyega Oyetola. Kazalika, gwamnatin jihar ta wajabtawa Ma'aikatar Watsa Labarai wallafa rahoton takardar gwamnatin a mujjalar gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel