Radadin Cire Tallafin Fetur: Abba Ya Fara Rabon Kayan Abinci Ga Ma’aikatan Kananan Hukumomin Kano
- Gwamnatin Abba a jihar Kano ta fara rabon tallafin kayan abinci ga ma'aikatan kananan hukumomi don rage radadin janye tallafin man fetur
- Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara na jihar Sani Danbatta ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis
- Kayan tallafin sun hada da shinkafa da masara, kuma ma'aikata a matakin albashi na GL 01 zuwa 06 ne za su fara samu a rukinin farko
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano, ta fara rabon kayan abinci ga ma'aikatan kananan hukumomin jihar domin rage masu radadin cire tallafin man fetur.
Tunda ya karbi mulki a 2023, shugaban kasa Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa tsadar kayan masarufi da shi kansa man fetur din.
A cikin wata sanarwa da dauke da sa hannun Sani Bala Danbatta, shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara ta jihar, ya ce ma'aikata sun fara samun tallafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shinkafa da masara ake rabawa ma'aikatan
Sani Danbatta ya ce:
"A kokarin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na rage wa ma'aikatan jihar radadin janye tattalin arziki, gwamnati ta fara raba tallafin kayan abinci ga kananun ma'aikatan jihar.
"Za a fara ba ma'aikata daga matakin albashi na GL 01 zuwa 06, daga ma'aikatu da hukumomi daban-daban na jihar, kuma wannan shi ne rukuni na farko."
Shugaban hukumar REB ya ce kayan tallafin sun hada da shinkafa da masara, kuma rabon kayan na gudana ne karkashin kulawar shugaban ma'aikata na jihar.
Doka ta haramta yin kayan daki da lefe a Kano
A wani labarin kuma, Barista Abba Hikima ya ce akwai wata doka da ta haramta duk wasu tsarabe-tsarabe na aure a jihar Kano.
Ya ce dokar ta haramta yin kayan lefe, kayan daki, kayan na gani ina so, da sauran abubuwan da ake yi a aure wanda ba addini ne ya tilasta yin su ba.
Lauyan ya ce idan aka kama mutum da karya wannan dokar, kotu na iya daure shi a gidan kaso, ko a ci shi tara ko kuma a hada masa duka biyun.
Asali: Legit.ng