‘Zunuban’ Emefiele da Yana Gwamnan Bankin CBN da Suka Jefa Shi a Matsala Yau
- Godwin Emefiele yana yawo tsakanin kotuna da gidan gyaran hali bayan dakatar da shi daga bankin CBN
- Tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya ya yi shekaru 9 a ofis, a sanadiyyarsu ake bincikensa
- An taso Emefiele ya yi bayanin abubuwan da suka faru a lokacinsa tsakanin Yulin 2014 zuwa Yulin 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Goodluck Jonathan ya kawo Godwin Emefiele ya zama gwamnan CBN a sakamakon dakatar da Muhammadu Sanusi II.
Godwin Emefiele ya yi sa’a a ofis, shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adinsa a matsayin gwamnan babban banki.
A yau hukuma ta taso Emefiele a gaba, Punch ta kawo rahoton yadda aka samu matsala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su menene laifin Godwin Emefiele?
1. Raguwar kudin waje
Kafin Godwin Emefiele ya dade a matsayin gwamnan CBN, $5,183,866,731 suka ragu a asusun kudin kasar wajen Najeriya a shekarar 2015.
2. Haramcin kawo wasu kayan waje
Karancin kudin waje ya tilastawa bankin CBN haramta bada kudin kasashen waje domin shigo da wasu kaya 43 kafin a halatta a 2023.
3. Shiga siyasa da yunkurin takara
A lokacin Emefiele an zargi babban bankin da tsoma baki a harkar siyasa a karshe sai ga shi ana zargin yana neman tikitin takarar shugaban kasa.
4. Canjin Naira
A Oktoban 2022, gwamnan bankin ya sanar da sababbin tsare-tsare, daga ciki akwai canjin manyan Nairori, kusan har yanzu ba a dawo daidai ba.
5. Sababbin tsare-tsaren cire kudi
CBN ya takaita cire kudi a bankuna da nufin yakar ta’addanci da magudin zabe, a karshe aka gurgunta tattalin arziki tare da jefa al’umma a wahala.
6. Tsare-tsaren noma
Bankin CBN a lokacin Emefiele ta maida hankali a kan harkar noma da nufin samar da abinci, amma ana zargin an tafka barna da sunan tsarin.
7. Bashi ga gwamnati
Ana zargin babban banki da buga tiriliyoyin kudi a ba gwamnati a matsayin bashi, a wajen yin hakan masana sun tabbatar da an sabawa dokokin CBN.
8. Farashin kudin waje
An yi shekaru ana da farashi dabam-dabam wajen saye da saida kudin waje, hakan ya hana Dala tashi sosai, amma ana zargin ya kawo rashin gaskiya.
Tashin Dala a Najeriya
Rahoto ya zo cewa Naira ta yi raunin da ba ta taba yi ba tun da Najeriya ta koma kan mulkin dimokradiyya kamar a lokacin Mista Godwin Emefiele.
Daga lokacin Joseph Sanusi, Charles Soludo har zuwa Sanusi Lamido Sanusi, Naira ta rasa N56 ne kawai a kan dalar Amurka a tsawon shekaru 16.
Asali: Legit.ng