Farfesa Soyinka Zai Fito da Sunayen ‘Yan APC da Ya Kamata EFCC, ICPC Su Cafke
- Akwai wasu da ya kamata hukumomin yaki da rashin gaskiya su cafke su domin ayi bincike a kan su
- Wole Soyinka ya ce nan gaba zai fadi wadanda ya dace a bincike su saboda mukaman da suka rike
- Alakar Farfesan da Bola Tinubu lokacin gwagwarmayar NADECO ba za ta hana shi taso shi a gaba ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Ogun - Wole Soyinka ya ce akwai wasu ‘yan siyasa a jam’iyyar APC mai mulki da ya kamata hukumomi suyi bincike a kan su.
Farfesa Wole Soyinka a hirarsa da tashar Channels a jiya ya ce akwai bukatar EFCC da ICPC su karkato akalarsu a kan ‘yan APC.
Marubucin yana ganin zai yi kyau EFCC mai yaki da rashin gaskiya da ICPC da ke yakar barayi ta binciki jiga-jigan jam’iyya mai-ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shahararren masanin yake cewa idan lokaci ya yi, zai fallasa ‘yan siyasar da ya dace hukumomin EFCC da ICPC su bi ta kansu a kasar.
Alakar Tinubu da Soyinka a NADECO
Guardian ta rahoto Soyinka yana cewa akwai ‘yan APC da ya kamata a binciki abubuwan da suka aikata sa’ilin da suka rike mukami.
A hirar da aka yi da shi, Soyinka ya tuna da irin gwagwarmayar da aka yi da Bola Tinubu a lokacin yana kungiyar NADECO a zamanin soji.
Duk da tarayyarsa da shugaban kasar na yanzu wajen yakar Janar Sani Abacha, Soyinka ya ce ba zai bari wannan ya rufe masa ido ba.
Farfesan yake cewa ba zai zura ido ana tafka rashin gaskiya ba saboda alakar NADECO.
Soyinka zai hada EFCC da ICPC da aiki
"Alal misal, idan lokaci ya yi, zan duba mutanen da ke cikin gwamnatinsa (Tinubu) wadanda ya kamata ayi shari’a da su a kotu, amma suna rike da muhimman mukamai a jam’iyya mai mulki"
"Shin suna amsa tambayoyi daga EFCC? Wane da wane da suka rike mukamai suna da garkuwa a lokacin, yanzu ba su da garkuwa"
"ICPC, EFCC, me ku ke yi a game da su? Meya faru? Muna jira.”
Wole Soyinka da zargin zaben 2023
An rahoto Wole Soyinka ya ce an shirya makarkashiya tun farko kafin takarar bara domin a tabbatar da ba ayi zaben na 2023 ba.
A lokacin da Farfesa Soyinka ya ziyarci Bola Tinubu a Legas, ya ce ba zai ce komai a kan gwamnatinsa ba sai ya shekara guda a ofis.
Asali: Legit.ng