Tashin Hankali Yayin da Mutanen Kauyuka 10 Suka Tsere Daga Gidajensu a Zamfara, An Fadi Dalili

Tashin Hankali Yayin da Mutanen Kauyuka 10 Suka Tsere Daga Gidajensu a Zamfara, An Fadi Dalili

  • Mazauna ƙauyuka 10 a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu kan fargabar harin ƴan bindiga
  • Mutanen dai sun bar gidajensu ne bayan sojoji sun shiga dajin dake iyaka da su sun ƙwato shanu a hannun wani shugaban ƴan bindiga
  • Tun da farko shugaban ƴan bindigan ya yi musu gargaɗin farmakarsu idan sojoji suka sake ƙwace masa shanu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Mazauna ƙauyuka 10 da ke ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu saboda fargabar harin wani hamshaƙin shugaban ƴan bindiga, Dan Nagala.

Dan Nagala dai a baya ya aike da barazanar kai hari ga mutanen waɗannan ƙauyukan.

Mutane sun bar gidajensu a Zamfara
Mutanen kauyuka 10 sun gudu daga gidajensu a Zamfara Hoto: @Mfaarees
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Gidan Soro, Maje, Fanda Hakki, Hayin Dankaro, Doka, Dan Gamji, Galmuwar Hannu, Dan Katsina, Dakwalge da Gidan Arne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun afkawa kauyuka 10 a karamar hukuma a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa mutanen suka bar gidajensu?

Mazauna yankin sun gudu daga gidajensu ne bayan wani samame da sojojin rundunar 'Operation Hadarin Daji' suka kai a baya-bayan nan, rahoton Business Day ya tabbatar.

A ranar Talatar da ta gabata ne jami’an sojojin suka kai farmaki dajin Danbasa-Buzaya inda suka ƙwato shanu masu yawan gaske da ake zargin Dan Nagala ya sato ya ajiye a dajin.

Wani mazaunin ƙauyen Gidan Soro, wanda buƙaci a sakaya sunansa, ya ce makonni uku da suka wuce sojoji sun je dajin sun ƙwato shanun da Dan Nagala ya sato masu yawa.

A kalamansa:

"Bayan faruwar lamarin, Dan Nagala ya gargadi mazauna ƙauyukan da ke kusa da dajin cewa, idan sojoji suka koma cikin dajin suka tattara masa 'shanunsa’, zai kai hari a duk ƙauyukan da ke kan iyaka da dajin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa cikin dare a jihar Neja

"Sojojin sun je dajin a ranar Talata sun ƙwato shanu da dama. Muna tsoron Dan Nagala zai iya kai hari a kowane lokaci kamar yadda ya yi alƙawari, shi ya sa muka gudu daga gidajenmu. Mun san mutumin, ba ya da imani, ba ya daraja rayuwar ɗan adam.
"Zan iya faɗa muku da ƙwarin gwiwa cewa saboda waɗannan shanu, Dan Nagala na iya shafe duk ƙauyukan da ke kusa da dajin."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji, Kyaftin Ibrahim Yahaya, kan lamarin, ya bayyana cewa ba zai iya cewa komai ba domin yana wajen wani aikin kakkaɓe ƴan bindiga a yankin Dan Jibga.

"Ku yi haƙuri a yanzu haka ina aikin kakkaɓe ƴan bindiga a yankin Danjibga. Ba zan iya ba da amsa ba, don Allah."

Wasu Jami'an Tsaro Na Taimakon Ƴan Bindiga, Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau ya yi zargin cewa akwai wasu jami'an tsaro dake taimakawa ƴan bindiga.

Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana cewa tuni wasu jami'an tsaro suka zama wakilan ƴan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng