Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar da Ake Ji da Ita a Jihar Kaduna

Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar da Ake Ji da Ita a Jihar Kaduna

  • An shiga jimami a jihar Kaduna bayan mummunar gobara ta tashi a kasuwar Panteka da ke Kaduna
  • Gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe 1:00 na dare ta shafi sashen ƴan katako da ke a fitacciyar kasuwar
  • Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ba a samu asarar rai ba a dalilin tashin gobarar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna a ranar Laraba ta tabbatar da aukuwar gobara a babbar kasuwar Panteka da ke Kaduna.

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna, Mista Paul Aboi, ya bayyana cewa gobarar ta shafi ɓangaren ƴan katako na kasuwar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Nasarawa: Fargaba yayin da matasan PDP suka aika muhimmin sako ga Kotun Koli gabannin yanke hukunci

Gobara ta shi a jihar Kaduna
An samu tashin gobara a kasuwar Panteka da ke Kaduna Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

Aboi ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga wani Mista Sadiq Mohammed, wanda ya garzaya hukumar da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, Aboi ya ce ba a samu asarar rayuka ko jikkata ba a sanadiyyar tashin gobarar.

A cewarsa, har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba saboda ana ci gaba da gudanar da bincike.

Yadda gobarar ta tashi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, shugaban sashen ƴan katako na kasuwar Mohammed Abubakar, ya ce gobarar ta fara ne da ƙarfe 1:10 na dare, ya kuma yabawa hukumar kashe gobara da ta ɗauki matakin gaggawa.

A kalamansa:

"Hukumar kashe gobara ta yi ƙoƙari wajen kashe gobarar, kuma bayan an kashe gobarar, ƴan kwana-kwana sun tsaya don taimakawa ƴan kasuwa ceto abin da ya rage har zuwa ƙarfe 8:00 na safe."

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da yan gida daya mutum 7 suka mutu sakamakon gobara a Kano

Abubakar ya ce, har yanzu ba a tantance asarar da gobarar ta jawo ba, ya ƙara da cewa an kafa kwamitin da zai tantance hakikanin asarar da aka yi ta fuskar kuɗi a gobarar.

A cewarsa:

"Muna kira ga hukumomin gwamnati da ƴan Najeriya masu hannu da shuni da su kawo mana agaji."

Gobara Ta Laƙume Kayayyakin Miliyoyi a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata gobara ta laƙume kayayyakin da darajarsu ta kai N80m a yankin Gezawa na jihar Kano.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Kazeem Sholadoye ya tabbatar da hakan inda ya ce an kuma ceto kayayyakin da darajarsu ta kai N300m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng