Kotu Ta Fara Yanke Hukunci Kan Shari’ar BBC da Wani Mawakin Kano
- Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta dage sauraron shari'ar da ake yi tsakanin wani mawakin Kano da BBC
- Mawakin mai suna Kamal Abdul ya shigar da sashen Hausa na BBC kara gaban kotu kan amfani da sautinsa ba tare da izini ba
- Mawakin ya nemi BBC ta biya shi naira miliyan 120 na amfani da sautin wakarsa ba bisa izini ba, abin da lauyan BBC ya kalubalanta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Wani mawaki dan jihar Kano, Abdul Kamal ya shigar da sashen Hausa na gidan rediyon Birtaniya (BBC) kara gaban babbar kotun tarayya da ke jihar Kano.
Mai shari'a N M Yunusa ya dage shari’ar zuwa ranar 12 ga Fabrairu, 2024.
Abin da ya jawo mawakin ya shigar da BBC kara kotu
Tun da fari, BBC ta kalubalanci bukatar Abdul Kamal na neman naira miliyan 120 daga kamfanin yada labaran bisa zargin yin amfani da sautin wakarsa ba tare da izininsa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ruwaito cewa Abdul Kamal ya kai karar sashen Hausa na BBC ne saboda amfani da sautin twakarsa a cikin shahararren shirinsu na 'Daga bakin mai ita' ba tare da izininsa ba.
BBC, a wata takarda da ta gabatar wa kotun, ta ce tun da Kamal ya bukaci a biya sa kudi, to babu bukatar kotun ta ba da umarnin dakatar da amfani da sautin wakarsa a shirinsu.
Yar majalisa ta yi murabus saboda satar jakar hannu
A wani labarin mai ban al'ajabi, wata 'yar majalisa a kasar New Zealand ta rubuta takardar murabus jim kadan bayan kama ta tana satar jakar hannu a wani kanti.
Faifan bidiyo ya nuna lokacin da 'yar majalisar mai suna Golriz Ghahraman ta sungumi jakar ta boye, lamarin da ta kira shi da "gurbatacciyar dabi'a da ta saɓa wa kyawawan halayenta".
Shugaban jam'iyyar Green Party zzz James Shaw ya ce 'yar majalisar ta dade tana fama da barazanar cin zarafi, kisa da tashin hankali, abin da ya ke tunani ya canja halayen Ghahraman.
Asali: Legit.ng