Daga-bakin-mai-ita: Sabbin bayanai sun bayyana game da ma'auratan da suka rabu saboda Buhari
Mahukuntan gwamnatin jihar Filato sun musanta labarin da gidan jaridar BBC Hausa ya wallafa na wasu ma'aurata Malam Abdullahi Yadau da ya saki matar sa mai suna Hafsat Suleiman a karamar hukumar Kanam saboda tace zata zabi Buhari a zaben nan mai zuwa.
Kamar dai yadda majiyar mu ta Daily Trust ta ruwaito cewa Kwamishinan yada labarai na jihar Yakubu Dati, ya bayyana labarin a matsayin kanzon kurege da makamancin sa ma bai faru ba.
KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci
Legit.ng Hausa ta tsinkayi cewa Kwamashinan Yakubu Dati yace: "A matsayin mu na gwamnati, munyi cikakken bayani game da lamarin bayan bullar labarin amma sai muka tabbatar da cewa ba haka bane ko kadan."
Ya kara da cewa su ma ma'auratan, an gayyace su zuwa ofishin 'yan sanda domin jin bahasi kuma sun tabbatar da cewa hakan bai faru ba kuma suna a tare ba saki.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin satin da ya gabata ne dai labarin ma'auratan yayi ta ruruwa kamar wutar jeji na wasu ma'aurata da suka rabu saboda sabanin siyasa.
Kamar dai yadda labarin ya zo, mijin dan gani kashenin dan takarar shugabancin kasar Najeriya a tutar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar ita kuwa matar sa tana matukar kaunar shugaba Buhari, dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC).
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng