Babbar Magana: Ƴan Bindigan da Suka Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali

Babbar Magana: Ƴan Bindigan da Suka Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali

  • Yan bindiga da suka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Ukum a jihar Benue sun nemi kuɗin fansa kafin sako shi
  • Wata majiya daga cikin dangi ta bayyana cewa maharan sun nemi N50m a matsayin fansar shugaban ƙaramar hukumar
  • Kwamishinan yaɗa labarai na Benue ya tabbatar da cewa ya ji kishin-kishin ɗin suna neman kudin fansa amma gwamnati na bakin kokarinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da shugaban riko na karamar hukumar Ukum a jihar Binuwai, Rabaran Haanongon Gideon, sun tuntubi ‘yan uwansa.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa masu garkuwa sun nemi iyalai da dangin ciyaman din su harhaɗa Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya rantsar da shugaban PDP a shirgegen muƙamin gwamnati, ya shiga taron FEC a Villa

Gwamna Alia na jihar Benuwai.
Yan bindigan da suka sace shugaban karamar hukuma a Benue Sun Turo sako Hoto: Governor Hyacinth Alia
Asali: Twitter

An yi garkuwa da Gideon tare da wasu mutane uku a ranar Asabar a kewayen Tongov na karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar a Arewa ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton babu tabbacin cewa kuɗin fansar da ƴan bindigan suka nema na ciyaman ɗin ne ko na sauran mutum ukun.

Majiyoyi a yankin sun ce an sace shugaban karamar hukumar ne tare da mataimakinsa kan harkokin mulki, Ior Silas Yuhwam, direbansa da kuma ɗan sanda.

Maharan sun yi awon gaba da su da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Asabar a Anyagba yayin da suke hanyar zuwa jana'izar babban basarake a ƙaramar hukumar Katsina-Ala, HRH Chief Fezaanga Wombo.

Masu garkuwa sun aiko saƙo mai ɗaga hankali

Wata majiya daga cikin iyalansa da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa masu garkuwan sun buƙaci N50m a matsayin kuɗin fansar shugaban ƙaramar hukuma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka mummunar ɓarna, sun sace mata sama da 35 tare da kashe rayuka a arewa

Haka kuma, wasu majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane na neman Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa.

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Kwamishinan yada labarai na jihar, Matthew Abo, ya shaidawa ƴan jarida ta wayar tarho cewa maharan sun nemi kudin fansa amma bai iya tantance adadin kudin ba.

A rahoton Tribune Online, Abo ya ce:

"Na ji cewa masu garkuwa da mutane na neman wasu makudan kudade duk da cewa ba zan iya tantance gaskiyar jita-jitar ba.
"Ba zan iya tabbatarwa ba amma gwamnatin jihar ta haɗa jami’an tsaro da ke aiki tukuru domin ceto shugaban.”

Tinubu ya ɗauki alƙawarin kawo karshen matsalar tsaro

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a ƙasa da ke ƙara taɓarɓarewa.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa ba zai huta ba har sai ya kawo ƙarshen duk wasu masu hannu kan matsalar rashin tsaron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262