Badakalar N438m: Ministan Tinubu Ya Ki Amsa Gayyatar Hukumar CCB? Gaskiya Ta Bayyana

Badakalar N438m: Ministan Tinubu Ya Ki Amsa Gayyatar Hukumar CCB? Gaskiya Ta Bayyana

  • An ce ministan harkokin cikin gida na Shugaba Bola Tinubu, Olubunmi Tunji-Ojo, ya buƙaci a sanya masa wata rana don gurfana a gaban hukumar ɗa'ar ma'aikata
  • Lamarin dai ya sabawa rahoton baya na cewa ministan ya yi watsi da gayyatar da hukumar ta yi masa don yi masa tambayoyi kan badaƙalar kwangilar N438m
  • Wata takarda da aka fallasa ta nuna cewa ministar jin ƙai Betta Edu da aka dakatar ta bai wa wani kamfani mai alaƙa da ministan kwangilar N438m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida na shugaba Bola Tinubu, Olubunmi Tunji-Ojo, ya buƙaci a sake sanya masa lokacin da zai bayyana a gaban hukumar ɗa'ar ma'aikata (CCB).

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar kula da da’ar ma’aikata

Tunji-Ojo zai bayyana gaban hukumar ne domin tattaunawa kan alaƙarsa da ɗaya daga cikin kamfanonin da suka samu kwangila daga ma’aikatar jin kai da yaƙi da talauci.

Tunji-Ojo ya aike da wasika zuwa ga hukumar CCB
Tunji ya bukaci CCB ta sanya masa sabuwar rana domin gurfana a gabanta Hoto: Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Twitter

Jaridar Nigerian Tribune ta ce ministan, wanda aka shirya zai bayyana a gaban CCB da ƙarfe 11 na safe a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya rubutawa hukumar wasiƙa, inda ya bukaci a sake sanya masa wata rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa Tunji-Ojo ya kasa gurfana a gaban CCB

An bayyana cewa Tunji-Ojo ya sanar da hukumar cewa yana da wani uzuri a hukumance, wanda ya buƙaci halarta, cewar rahoton The Nation.

Ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu wacce aka dakatar, ita ce ta bayar da kwangilar N438m ga wani kamfani mai alaƙa da Tunji-Ojo.

Wata takarda da aka fallasa ta nuna cewa kamfanin da ke da alaƙa da ministan harkokin cikin gida ya karbi N438m a matsayin kuɗin kwangila daga ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci.

Kara karanta wannan

"Shi ba dan jihar nan ba ne": Wike ya bayar da karin haske kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Tunji-Ojo ya musanta samun kwangila a hannun Betta Edu

Sai dai Tunji-Ojo ya musanta cewa yana da hannu a kwangilar, inda ya dage cewa ya daina shiga harkokin yau da kullum na kamfanin tun shekarar 2019 da ya ajiye muƙaminsa na darakta.

CCB ta gayyaci ministan a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 10 ga watan Janairu, wacce aka gani a ranar Litinin 15 ga watan Janairu cewa ya gurfana a gabanta a ranar Talata 16 ga watan Janairu domin amsa tambayoyi kan badaƙalar kwangilar.

Tinubu Ya Gayyaci Tunji-Ojo

A baya rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kira ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, zuwa fadarsa da ke Aso Rock a Abuja.

Shugaban ƙasar ya kira Tunji-Ojo ne bayan sunansa ya fito a badaƙalar kwangilolin da aka raba a ƙarƙashin ma'aikatar jin ƙai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng