Tinubu Ya Sanya Labule da Shugabannin Tsaron Najeriya Kan Dalili 1 Tak, Bayanai Sun Fito
- A yanzu haka Shugaba Tinubu ya na ganawa da manyan jami'an tsaron Najeriya a fadarsa da ke birnin Abuja
- Tinubu na ganawar ce musamman saboda yadda rashin tsaro ya yi kamari a birnin Abuja a 'yan kwanakin nan
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da yawan hare-haren 'yan bindiga ba a birnin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja -Shugaban kasa, Bola Tinubu yanzu haka ya na ganawar gaggawa da hafsoshin tsaron Najeriya.
Tinubu ya ganawar ce musamman saboda yadda rashin tsaro ya yi kamari a birnin Abuja a 'yan kwanakin nan.
Mene dalilin ganawar Tinubu da hafsoshin tsaron?
Duk da ba a san musabbabin ganawar ba, amma TheCable ta ruwaito cewa zaman bai rasa nasaba da yawan hare-haren 'yan bindiga a birnin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 5 ga watan Janiru 'yan bindiga sun kai farmaki yankin Bwari inda suka yi garkuwa da wasu mata shida 'yan gida daya.
Har ila yau, maharan sun kuma yi garkuwa da wasu da dama a yankin wanda hakan ya jawo cece-kuce a kasar, cewar TheNewsGuru.
Yadda mahara suka addabi birnin Abuja
Daga bisani maharan sun hallaka daya daga cikinsu mai suna Nabeena bayan rashin biyan kudin fansa har naira miliyan 60.
Farfesa Isa Ali Pantami a ranar Lahadi 14 ga watan Janairu ya ce ya samu wani abokinsa wanda ya yi alkawarin biyan kudin fansa ga 'yan bindiga.
Har ila yau, bayan wannan alkawari da ya yi, 'yan bindigar sun sake hallaka wasu mutum uku da ke hannunsu bayan sun kara kudin fansar.
Wike ya sanya labule da masu ruwa da tsaki
A wani labarin, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sanya labule da masu ruwa da tsaki da ke birnin Abuja a yau Talata 16 ga watan Janairu.
Wike ya shiga ganawar ce kan matsalar rashin tsaro da ya yi kamari a birnin Abuja a kwanakin nan.
Birnin Abuja na fama da hare-haren 'yan bindiga wanda ya yi sanadin rayukan wasu da dama ciki har Nabeena da suka hallaka.
Asali: Legit.ng