Kaduna: Masu Garkuwa Sun Tsare Tsohon Shugaban Makaranta da Ya Tafi Kai Kudin Fansar Wani

Kaduna: Masu Garkuwa Sun Tsare Tsohon Shugaban Makaranta da Ya Tafi Kai Kudin Fansar Wani

  • Sanata Shehu Sani ya ba da labarin wani tsohon shugaban makaranta da yan bindiga suka kama yayin da ya ke kai kudin fansar wani
  • Lamarin ya faru a Birnin Gwari, jihar Kaduna inda Sani ya ce kwanaki uku kenan tsohon shugaban makarantar na a tsare
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kira iyalan malamin, sun nemi kudin fansa kafin shi ma su sako shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - An shiga tashin hankali a Kaduna yayin da 'yan bindiga suka yi garkuwa da wani tsohon shugaban makaranta lokacin da ya ke kai kudin fansar wani da 'yan bindigar suka sace.

Sanata Shehu Sani ya tabbatar da faruwar hakan a ranar Talata, yana mai nuna damuwa kan karuwar hare-haren 'yan bindiga da ayyukan masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu zai kawo karshen rashin tsaro a cikin watanni 6 Inji Janarorin Soja

Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin makaranta a Kaduna
Masu garkuwa sun tsare wani tsohon shugaban makaranta da ya je kai masu kudin fansa. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Tsohon malamin makarantar ya ke kai kudin fansar wani da aka kama a Birnin Gwari lokacin da masu garkuwar suka tsare shi shima, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun nemi kudin fansa daga iyalan tsohon malamin

Tsawon kwanaki uku ne masu garkuwar na tsare da shi, kuma sun kira iyalansa a waya tare da neman kudin fansa kafin su sake shi.

Sani ya wallafa labarin a shafinsa na X, inda ya ce:

"Wani tsohon shugaban makaranta ya amince ya kai kudin fansar wani da 'yan bindiga suka kama a Birnin Gwari, jihar Kaduna.
"Amma yanzu kwana uku ke nan sun tsare shi, sun kira iyalansa suna so a biya su kudin fansa kafin su sake shi."

Ga abin da ya rubuta:

Halin da al'ummar Birnin Gwari su ke ciki kan matsalar tsaro

Kara karanta wannan

Satar mutane a Abuja: "Mun kama wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri", Wike ya yi karin bayani

Yin garkuwa da tsohon shugaban makaranta ya cusa tsoro a zukatan mazauna garin Birnin Gwari, garin da dama suka dade suna fama da masu garkuwa da 'yan fashin daji.

Wani mazaunin Birnin Gwari, Alhassan Aminu ya shaidawa Legit Hausa cewa, kusan kullum suna kwana ne a cikin fargabar hari daga 'yan bindiga.

Kowa na fargabar zuwa kai wa 'yan bindiga kudin fansa

Mallam Aminu ya ce a duk lokacin da aka hada kudi za a kai wa 'yan bindiga, kowa na tsoron zuwa don gudun kar su tsare shi kamar yadda suka yi wa tsohon malamin.

Ya ce:

"Haka muke kwana muke tashi cikin fargaba, suna iya shigo mana a duk lokacin da suka ga dama. Tun 'yan sa kai ka tabuka wani abu, har ta kai sai dai mu fawwala wa Allah komai.
"Kowa na jin tsoro idan aka ce ya je ya kai kudin fansa, saboda shi ma zai iya shiga komarsu. Lallai muna rokon gwamnati da jami'an tsaro su kawo mana dauki a ƙauyukan Birnin Gwari."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari kauyen Zariya, sun sace uwa da ɗanta, mijin ya tsere

Yan bindiga sun sake kashe wata daliba bayan kashe Nabeeha

A wani labarin kuma, an samu karin bayani kan wata daliba mai suna Mis Folorunsho Ariyo da 'yan bindiga suka kashe ta tare da Nabeeha Al-Kadriyar a Abuja.

An ruwaito cewa 'yan bindiga sun sace Folorunsho tare da mahaifiyarta da'yan uwanta guda uku makonnin biyu da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.