Atiku Ya Bayyana Abin da Ya Hana Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Kasar Nan, Ya Fadi Mafita

Atiku Ya Bayyana Abin da Ya Hana Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Kasar Nan, Ya Fadi Mafita

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan matsalar rashin tsaro a ƙasar nan
  • Atiku ya ɗora alhakin rashin kawo ƙarshen matsalar a kan talauci da yunwa da suka yi wa mutane katutu
  • Ya buƙaci hukumomi da su tashi tsaye domin ganin sun kawo ƙarshen matsalar wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ɗora laifin yawaitar garkuwa da mutane da rashin tsaro a ƙasar nan kan abinda ya bayyana a matsayin ƙara taɓarɓarewar talauci da yunwa a ƙasa.

A ranar 5 ga watan Janairu ne wasu ƴan bindiga suka sace wasu ƴan mata guda shida a ƙaramar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin jama’a.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Atiku ya yi magana kan rashin tsaro
Atiku ya fadi dalilin tabarbarewar tsaro a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A ranar Juma'a da ta gabata, masu garkuwa da mutane sun kashe Nabeeha, ɗaya daga cikin mata shida da suka sace, domin gargaɗi ga iyayenta da suka kasa biyan kuɗin fansa N60m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya magantu kan rashin tsaro

Da yake mayar da martani a wani jawabi a shafinsa na X a ranar Litinin, Atiku ya ce yawan tashe-tashen hankula a ƙasar nan na damunsa.

A kalamansa:

"A bayyane yake cewa talauci da yunwa da ke ƙara ta’azzara a ƙasa na ƙara ta’azzara matsalar garkuwa da mutane da rashin tsaro a Najeriya, musamman a Abuja, babban birnin tarayya.
"A lokacin da gwamnati ta kasa sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa, gayyata ce ga masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata muggan laifuka don su samu damar ziyartar gidaje da otal-otal a cikin birane da kewaye, suna garkuwa da ƴan ƙasa ba tare da turjiya ba. Wannan abun takaici ne."

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin kisan Nabeeha yan bindiga sun sace daliban jami'a a Katsina

Ya koka da yadda masu garkuwa da mutane ke ci gaba da mulkinsu na ta’addanci ba tare da an shawo kan matsalar ba, yana mai kira ga hukumomi da su magance matsalar tsaro cikin gaggawa domin dawo da yardar ƴan Najeriya.

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Jami'a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata guda biyu na jami'ar Al-Qalam da ke jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne a lokacin da suke kan hanyar komawa makaranta daga jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng