Rashin tsaro: Wike Ya Shiga Ganawa Babu Shiri da Masu Ruwa da Tsaki a Abuja, Bayanai Sun Fito
- Yayin da rashin tsaro ke kara kamari, Ministan Abuja ya shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki
- Wike na jagorantar ganawar ce da manyan shugabannin jami'an tsaron birnin da masu sarautar gargajiya
- Wannan na zuwa ne yayin da rashin tsaro ke kara kamari a birnin Abuja da kewaye musamman a wannan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki a birnin Abuja.
Wike ya na ganawar ce da manyan jami'an tsaron birnin Abuja da masu sarautar gargajiya da kuma masu rike da hukumar FCTA.
Mene dalilin Wike na shiga ganawar gaggawa?
Wannan na zuwa ne yayin da rashin tsaro ke kara kamari a birnin Abuja da kewaye musamman a wannan lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke magana a ganawar, Wike ya ce samar da tsaro ga mazauna birnin shi ne babban abin da ya sanya a gaba.
Ya ce gwamnati na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da samar da tsaro da kare lafiyar al'umma, cewar Daily Trust.
Wane gargadi Wike ya yi kan matsalar tsaro a Abuja?
Ministan ya hori shugabannin kananan hukumomi a birnin da su himmatu wurin sauke nauyin da aka daura musu.
Ya bukaci jami'an tsaro da su kara himma da kuma kawo wasu sabbin tsare-tsare don dakile matsalar a jihar, kamar yadda Daily Post ta tattaro.
'Yan bindiga su na cin karensu babu babbaka a birnin musamman a cikin 'yan kwanakin nan bayan hallaka wata daliba saboda rashin biyan kudin fansa.
Pantami ya nuna takaici kan rashin tsaro a Najeriya
A wani labarin, Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar tsaro ke kara kamari.
Pantami ya ce ya na jin takaici yadda ya kawo tsari amma aka yi watsi da shi a yaki da ta'addanci a kasar.
Ya kara da cewa an sha masa barazanar rayuwa daga mutane da hukumomi kan tsarin amma kuma bai cimma burinsa ba.
Asali: Legit.ng