Ali Ya Ga Ali: Tinubu Ya Hadu da Obasanjo Karo Na Farko Tun Bayan Zaben 2023, Hoto Ya Bayyana

Ali Ya Ga Ali: Tinubu Ya Hadu da Obasanjo Karo Na Farko Tun Bayan Zaben 2023, Hoto Ya Bayyana

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo sun hadu a karo na farko tun bayan zaben 2023
  • Haduwa ta karshe tsakanin dattawan biyu ta kasance tun a watan Agustan 2022, a garin Abeokuta lokacin da Tinubu ya je domin yakin neman zabensa
  • Obasanjo dai ya goyi bayan dan takarar jam'iyyar Labour party, Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo sun hadu a wajen rantsar da Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo.

An dai rantsar da Uzodimma ne a matsayin gwamnan jihar Imo a karo na biyu a garin Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya karbi rantsuwar kama aiki karo na biyu a gaban jiga-jigai, bayanai sun fito

Tinubu ya hadu da Obasanjo a Imo
Ali Ya Ga Ali: Tinubu Ya Hadu da Obasanjo Karo Na Farko Tun Bayan Zaben 2023, Hoto Ya Bayyana Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Wannan ita ce karo na farko da shugabannin biyu ke haduwa tun bayan babban zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haduwar karshe da dattawan biyu suka yi ya kasance a lokacin da Tinubu ya ziyarci Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar 17 ga watan Agustan 2022, yayin yakin neman zaben shugaban kasa.

Sai dai kuma, Obasanjo ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ne a zaben amma ba Tinubu ba.

Peter Obi dai shi ne Wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa na 2023, Bayan Atiku Abubakar na jamiyyar PDP da ya zo na biyu.

Mai bai wa shugaban kasar shawara a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @aonanuga1956, cike da al'ajabin abun da ke yawo a zukatansu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa Imo domin rantsar da Uzodimma

Gwamna Uzodinma ya karbi rantsuwar aiki

A baya Legit Hausa ta kawo cewa Gwamna Hope Uzodinma ya karɓi rantsuwar kama aiki a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Imo watanni kadan bayan nasarar da ya samu a zaben gwamna.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an rantsar da gwamnan ne da karfe 3:24 na rana a filin wasa na Dan Ayiam da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Taron rantsar da gwamnan wanda aka yi ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2023 ya samu halartar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng