EFCC Ta Kama Tsohon Minista da Shugaban Wani Kamfani Kan Zargin Hannu a Damfarar N3.6bn

EFCC Ta Kama Tsohon Minista da Shugaban Wani Kamfani Kan Zargin Hannu a Damfarar N3.6bn

  • Tsohon minista a Najeriya ya shiga hannun hukumar EFCC bisa zargin hannu a damfarar rancen kudi N3.6bn
  • Hukumar EFCC ta kama Charles Chukwuemeka Ugwuh da shugaban kamfanin Ebony Agro Industries Ltd a Owerri jihar Imo
  • Mai magana da yawun EFCC ya bayyana cewa za a gurfanar da su a gabam ƙuliya da zaran an kammala bincike kan zargin da ake musu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) ta cafke tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Charles Chukwuemeka Ugwuh.

EFCC mai yaƙi da masu rashawa a Najeriya ta damƙe tsohon ministan ne bisa zarginsa da hada baki da k]ma damfarar rancen kudi kimanin Naira biliyan 3.6.

Kara karanta wannan

Tunji Ojo: Gwamnati ta shiga binciken Ministanta da ake zargi a badakalar kwangila

Jami'an EFCC sun damƙe tsohon minista.
EFCC Ta Cafke Tsohon Minista Kan Zargin Rancen Damfara Na N3.6bn Hoto: @duso4me
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar yaƙi da cin hanci EFCC, Dele Oyewale, ya fitar kuma hukumar ta wallafa a X watau Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta ce an kama tsohon ministan ne tare da Cif Geoffrey Ekenma a ranar 11 ga Janairu, 2024, a lamba 2, Musa Yar Adua Way, New Owerri, jihar Imo.

Meyasa EFCC ta kama tsohon ministan?

Hukumar ta ce an kama mutun biyun ne biyo bayan, "ƙorafin da wani banki ya kai EFCC kan zamba da ake zargin wani kamfani mai suna Ebony Agro Industries Ltd. mai alaka da tsohon ministan."

Sanarwan ta ce:

"Bincike ya nuna Ugwuh da Ekenma, Manajan darakta na kamfanin Ebony Agro Industries Ltd., sun karɓi bashi daga bankin domin saye da samar da shinkafa."

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Matawalle da sauran tsaffin gwamnoni 13 da EFCC ta sake waiwayar zargin badakala kansu

“Amma waɗanda ake zargin, a cewar mai shigar da korafin, sun kasa cika hakki da sharaɗin da ya dace a bankin, kuma duk kokarin da aka yi na ganin sun biya bashin kudin ya ci tura."

Daga karshe, kakakin EFCC ya bayyana cewa hukumar za ta gurfanar da waɗanda ake zargin da zaran an kammala bincike da tattara hujjoji.

Gwamnan APC Ya Shirya Liyafa Bayan Nasara a Kotun Koli

A wani rahoton kuma Gwamnan Ebonyi ya godewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan samun nasara a kotun koli.

A wurin wata liyafar murna ranar Lahadi, Gwamna Nwifuru ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa zai musu hidima cikin gaskiya da ƙauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262