Shugaba Tinubu Ya Isa Imo Domin Rantsar da Uzodimma

Shugaba Tinubu Ya Isa Imo Domin Rantsar da Uzodimma

  • Yanzu nan shugaba Tinubu ya isa jihar Imo domin halartar bikin rantsar da gwamnan jihar Hope Uzodimma a mulkinsa karo na biyu
  • Shugaba Tinubu dai ya fara halartar taron bikin tunawa da 'yan mazan jiya, daga bisani ya wuce zuwa jihar ta Imo
  • Tinubu ya samu rakiyar wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa, kuma ya samu tarbar Gwamna Uzodimma a filin jirage na Sam Mbakwe a Owerri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Imo - Shugaba Bola Tinubu ya dira Owerri babban birnin jihar Imo domin bukin rantsar da Gwamna Hope Uzodimma a mulkinsa na biyu a jihar.

Tinubu wanda ya fara halartar taron bikin tunawa da 'yan mazan jiya na shekarar 2024 da aka gudanar a Abuja, ya dira Owerri misalin karfe 1:00 na ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da N-Power, Tinubu ya dauki matakin karshe kan shirin NSIPA, ya fadi dalili

Tinubu ya isa Imo don rantsar da Uzodimma
Yanzu: Tinubu ya isa jihar Imo don rantsar da Uzodimma, an samu karin bayani. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Tunubu zai kaddamar da ayyuka a Owerri, jihar Imo

Gwamna Hope Uzodimma da mukarrabansa suka tarbi Shugaba Tinubu a filin jiragen sama na Sam Mbakwe, kamar yadda Dada Segun, hadimin Tinubu kan kafofin sada zumunta ya sanar a shafinsa na Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya samu rakiyar wasu daga cikin jami'an gwamnati, kuma zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar bayan kaddamar da babban filin wasanni na Dan Anyiam da ke Owerri.

Ga abin da Segun ya rubuta:

Baya ga Shugaba Tinubu, wasu gwamnoni da suka hada da Chukwuma Soludo sun halarci taron rantsar da Uzodimma.

Channel TV ta ruwaito cewa mataimakiyarsa Valentine OnyekaChukwu Ibezim ce ta wakilci gwamnan jihar Anambra.

Karashen labarin na zuwa...

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.