Batun Sace ’Yan Matan Abuja: Peter Obi Ya Koka Kan Yadda ’Yan Najeriya Suka Rasa ’Yanci

Batun Sace ’Yan Matan Abuja: Peter Obi Ya Koka Kan Yadda ’Yan Najeriya Suka Rasa ’Yanci

  • Peter Obi ya bayyana fushi da bacin rai bayan samun labarin kisan da aka yiwa wata dalibar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria
  • An sace ‘yan mata tare da mahaifinsu a Abuja, lamarin da ya dauki hankalin al’ummar kasar nan a makon da ya gabata
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da alkawarin kare rayuka da lafiyar ‘yan kasar da ke halin ha’ula’i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yiwa Nabeeha Al-Kadriyar, daya daga cikin ‘yan uwa matan da aka sace a Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, inda ta kara da cewa satar ta nuna rashin tsaro a Najeriya da kuma rashin kula da halin ‘yan kasarta.

Kara karanta wannan

Da an hana Abba Gida-Gida mulkin Kano, da Najeriya ta kama da wuta, inji Buba Galadima

Peter Obi ya caccaki gwamnati kan mutuwar Nabeeha
'Yan Najeriya sun rasa gata, inji Peter Obi | Hoto: @affantech1, @PeterObi
Asali: Twitter

Bayanin kuka daga Peter Obi kan kisan Nabeeha:

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Bayan rahoton kisan da aka yi wa Nabeeha Al-Kadriyar dalibar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, wadda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita tare da mahaifinta da ‘yan’uwanta a Abuja, hakan ba wai kawai ya nuna yadda rashin tsaro ya addabi al’umma a halin yanzu bane, har ta lao ga nuna yadda Najeriya ke cikin yanayin rashin kula da hatsari.
“Tashin hankalin ga ahalin ke fama da shi da kuma jinin wannan yarinyar da ta ji ba bata gani ba ya kamata ya zama darasi ga shugabanni, wadanda aikinsu shi ne kare ran kowane dan Najeriya.
“Kasancewar wadannan sace-sace da kashe-kashe da sauran rahotanni na fashi da makami da kuma hare-haren ta’addanci, yanzu haka suna faruwa a Abuja, babban birnin kasar, ya nuna karara kan yadda sauran sassan kasar ke cikin rashin tsaro ainun.”

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

An sace wasu fasinjoji a jihar Benue

A wani labarin, akalla fasinjoji 45 ne a cikin wasu manyan motocin aka sace a Orokam da ke kan hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Ogbadigbo ta jihar Benue, Vanguard ta ruwaito.

Shedun gani da ido da wani direba a garin Makurdi da ya tsallake rijiya da baya tare da fasinjoji, sun bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Alhamis.

An ruwaito cewa, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai sun fito ne daga wani daji da ke Orokam, inda suka tursasawa direbobin cin burki da kuma tsayawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.