Ana Ci Gaba da Kuka Kan Sace ’Yan Mata a Abuja, ’Yan Bindiga Sun Kuma Sace Wasu 45 a Benue

Ana Ci Gaba da Kuka Kan Sace ’Yan Mata a Abuja, ’Yan Bindiga Sun Kuma Sace Wasu 45 a Benue

  • Rahoton da muke samu daga jihar Benue ya bayyana cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sace mutane sama da 45 a wani yankin jihar
  • Jihar Benue na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ake yawan fuskantar sace-sacen al’umma a kasar da ke nahiyar Afrika
  • Ana ci gaba da kokarin samar da yadda za a kubutar da wasu ‘yan matan da aka sace a babban birnin tarayya Abuja a makon jiya

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Benue - Akalla fasinjoji 45 ne a cikin wasu manyan motocin aka sace a Orokam da ke kan hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Ogbadigbo ta jihar Benue, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Pantami ya samo wanda zai biya kudin fansa a sako 'yan uwan Nabeeha da aka sace a Abuja

Shedun gani da ido da wani direba a garin Makurdi da ya tsallake rijiya da baya tare da fasinjoji, sun bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Alhamis.

'Yan bindiga sun sace mutane 45 a Benue
An sace mutane 45 a Benue a makon jiya | Hoto: Benue Links Nig. Ltd
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya faru

An ruwaito cewa, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai sun fito ne daga wani daji da ke Orokam, inda suka tursasawa direbobin cin burki da kuma tsayawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, direban ya ce:

“’Yan ta’addan sun samu saukin tsayar da motocin ne saboda titin da ke wurin ya lalace ainun.”

Ya kuma bayyana cewa, ya ga wani marashi mai kananan shekaru daga cikin ‘yan ta’addan ne da ke rike da muggan makamai, Idoma Voice ta tattaro.

Hakazalika, ya shaida cewa, lamarin ya faru ne ido na ganin ido, inda yace mutane ne uku suka tsayar da motocin bas din tare da tara mutane da yawa, lamarin da ke nuna suna neman fansa mai tsoka.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Sojoji sun zo kawo dauki

Daya baya ne aka ce wasu sojoji sun zo yankin a kan babura da mota kirar Hilux, inda suke tambayar inda ‘yan ta’addan suka yi.

Da aka zanta da shugabannin kamfanin sufurin a tashar motar Wurukum, sun bayyana yadda tsagerun ke neman Naira miliyan 15 na fansa, inda daga baya suka tsaya a kan Naira miliyan 3 kan kowane mutum.

Ya zuwa yanzu dai an sanar da ahalin wadanda aka sacen, kana ana ci gaba da magana da ‘yan ta’addan don daidaita batun fansa.

An samu hanyar biyan fansan ‘yan uwan Nabeeha

A wani labarin na daban, farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda ya kawo hanyar sharewa ahalin Nabeeha hawaye bayan samo wanda zai biya kudin fansan da ‘yan bindiga suka nema bayan sace su.

Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan ta’adda suka yi awon gaba da wasu ‘yan gida daya ‘yan mata shida, inda suka nemi kudin fansan miliyoyin kudade.

Wannan lamari ya dauki hankalin ‘yan Najeriya da dama, musamman ganin ya faru ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya fi ko ina tsaro a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.