Wata ‘Yar Najeriya ta bar tarihi a Jami’ar Kasar India
- Wata ‘yar Najeriya mai suna Esther Ruby Daniel ta ciri tuta a kasar India
- Esther Ruby Daniel ta zo ta daya a wasannin da aka yi a Jami’ar Amity da ke Kasar India
- Ba tun yau wannan Yarinya ‘yar Najeriya ta fara cin wasanni ba
Wata ‘yar Najeriya ta shiga cikin littafin tarihi a Kasar India bayan da ta zo ta daya a wasanni da aka yi a Jami’ar Amity da ke Garin Haryana a Kasar India. Wannan ‘Yar Najeriya tana da shekaru 17 ne a duniya, sannan kuma tana aji biyu na karatu.
The Nation ta rahoto cewa ba tun yau wannan yarinya mai suna Esther Ruby Daniel ta fara samun nasara a wasannin Jami’ar ba, tun tana aji daya ta saba cin wasanni. Esther Daniel ta samu kyautar zinari a Gasar wasanni na daliban shari’a a watan ta na farko a makarantar.
KU KARANTA: Darajar Farashin Naira ya daga sama
Wannan yarinya ‘Yar Najeriya ta samu cin kyautar gwal a farkon shekarar nan a wajen gasar tseren mita 200. Haka kuma ta zo ta biyu a wasan dogon tsalle. Ko a wannan watan, ta samu lashe gwal a wajen tseren mita 100. Esther Ruby Daniel asalin ‘Yar Jihar Akwa-Ibom ce
Bayan taci gwal a Ranar Talata na wancan mako, wannan yarinya ta kara da zuwa na uku a Ranar Jumu’a da aka kara da sauran Jami’o’i. Yanzu an buga sunan ta a Jaridun Kasar India. Mahaifin ta yace yana alfahari da ita.
Asali: Legit.ng