Bayan Shiga Har Wata Kasa Da Kashe Mataimakin Shugaban Hamas, Isra’ila Ta Yi Awon Gaba Da Danginsa

Bayan Shiga Har Wata Kasa Da Kashe Mataimakin Shugaban Hamas, Isra’ila Ta Yi Awon Gaba Da Danginsa

  • Rahoto ya bayyana yadda kasar Isra’ila ta bayyana kame wasu mutanen da ke alaka da mataimakin Hamas da suka kashe kwanan nan
  • An ruwaito cewa, Isra’ila ta kame ‘yan uwan tare da tsare su a wani wuri, lamarin da ke kara daukar hankalin duniya
  • Ba yanzu aka fara kai hare-hare da kame Falasdinawa da gallaza musu azaba a hannun sojojin kasar Isra’ila da ke ci gaba da mamaye yankinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Ramallah - Sojojin gwamnatin Isra'ila sun kama wasu 'yan uwan Saleh al-Aruri, shugaban kungiyar Hamas da aka kashe a kasar Lebanon cikin wannan watan, kamar yadda majiyoyin Falasdinawa da sojojin Isra'ila suka sanar a ranar Lahadi, Arab News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Pantami ya samo wanda zai biya kudin fansa a sako 'yan uwan Nabeeha da aka sace a Abuja

Kisan da aka yi wa Aruri, mataimakin shugaban kungiyar Hamas, a wata unguwa da ke birnin Beirut a ranar 2 ga watan Janairu, ya dauki hankalin jama’a, musamman bangarorin siyasar duniya.

Sojojin Isra'ila sun ce a ranar Lahadi sun tsare matan biyu a yankin Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye bayan tunzura aikin ta'addanci kan kasar Isra'ila.

Yadda Isra'ila ta kame dangin shugaban Hamas
An kama dangon mataimakin shugaban Hamas | Hoto: @brecorder
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka kame aka kuma tsare

Surukin Aruri, Awar al-Aruri, ya ce matan biyu da wasu 'yan uwa da dama an tsare su a gidan yari, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kungiyar Palastinawa ‘yan fursuna, wata kungiyar gangamin neman ‘yanci ta ce Dalal al-Aruri mai shekaru 52 da Fatima al-Aruri mai shekaru 47 ne aka tsare a birnin Ramallah.

A tun farko, sojin Isra’ila sun hallaka babban mai fada a ji a kungiyar Hamas din ne bias zarginsa da hannu wajen kitsa harin da Hamas ta kaiwa Isra’ilawa a watan Oktoban bara.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Yadda Isra’ila ta kashe ‘yan Gaza da yawa

Ya zuwa yanzu, an kasha Falasdinawa da dama a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa mazauna Gaza da kewaye tsawon lokaci.

Kasashen duniya da dama na tofa bakin yawu ga halin Isra’ila, inda kawayenta kuwa ke ci gaba da ingiza ta wajen ci gaba da cin zarafin Falasdinawa.

Yadda aka kashe mataimakin shugaban Hamas

A wani labarin, harin da Isra’ila ta kai kan mazauna Beirut ta kasar Lebanon, ta yi ikrarin cewa, hari ne kan daya daga cikin shugabannin kungiyar hamayyarta Hamas, BBC News ta ruwaito.

Mark Reveg, mai magana da yawun Isra’ila ya ce, mataimakin shugaban Hamas, Saleh Al-Arouri ya mutu a wani harin da jirgin Isra’ila ya kai kan shugabannin Hamas.

Kungiyar Hamas dai ta yi Allah-wadai da wannan kisa na shugabanta, inda kawarta tace kai harin ma tun da fari wani yunkuri ne na takalar rikici a Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.