Yan Sanda Sun Kama Wani Hatsabibin Shugaban ’Yan Bindiga a Kasuwar Jihar Arewa
- Dubun wani shugaban 'yan bindiga ya cika bayan da 'yan sanda suka kama shi a kasuwar Tungar Mallam da ke jihar Neja
- Kwamjshinan 'yan sanda na jihar Neja ya ce an kama dan bindigar mai suna Rabee bayan bin diddigin sa da tattara bayanan sirri
- Haka zalika rundunar 'yan sandan jihar ta kama wasu 'yan ta'adda 14 da suka aikata laifukan da suka shafi garkuwa da mutane
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Neja - Rundunar 'yan sanda a jihar Neja sun cafke wani Rabiu Yusuf da aka fi sani da Rabee wanda ake zargin shugaban 'yan bindiga ne a yankin Paikoro da ke jihar.
Kwamishinan'yan sanda na jihar Shawulu Ebenezer Danmamman ne ya bayyana hakan inda ya ce an kama Rabee ne a babbar kasuwar Tungar Mallam.
Garuruwan da shugaban 'yan bindigar suke addaba
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan ya ce an kama Rabee ne a ranar 6 ga watan Janairu bayan samun bayan sirri, kuma ya amsa laifin yin garkuwa da mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya kara da cewa dan ta'addan na cikin dabar Muware wacce ke addabar garuruwan Beji, Maikunkule, Bosso, Gawu-Babangida, Sangeku, Bangi, Gulu da Lapai.
Yan sanda sun kama 'yan fashi da masu garkuwa 14
Ya ce rundunar ta kuma kama wasu 'yan ta'adda 14 da suka aikata laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, satar mota da dai sauran laifuka, jaridar Leadership ta ruwaito.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Abubakar Hussaini daga kauyen Anaba, sai Buba Mohammed daga kauyen Maje da Mainasara Muhammadu na kauyen Takalafiyax Ibeto-Nasko, sai kuma Ibrahim Abdullahi daga Kontagora.
Kwamishin ya ce an kama mutanen ne bisa laifin satar wani dan shekara 20 tare da karbar naira miliyan 1.6 matsayin kudin fansar sa.
Yan bindiga sun sace mutane 10 a Abuja
A wani labarin, 'yan bindiga sun shiga rukunin gidaje na Sagwari da ke Abuja, yankin Dutse inda suka yi awon gaba da mutane 10.
Yan bindigar sun sace mutanen ne a ranar Lahadin makon da ta gabata, kuma yi wa masu gadin rukunin gidajen dukan tsiya, kamar yadda wani ganau ya shaidawa manema labarai.
Asali: Legit.ng