Innalillahi: Mutane Sun Mutu Yayin da Motar Gwamnati Ta Yi Mummunan Hatsari, Gwamna Ya Magantu
- Mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya yayin da motar hukumar sufuri ta Katsina ta gamu da mummunan hatsari a hanyar Abuja
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya jajantawa iyalan waɗanda suka mutu a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar
- Ya ce gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen kare rayukan al'ummar jihar da tabbatar da irin haka ba ta ƙara faruwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya jajantawa iyalan wadanda hatsari ya rutsa da su da motar hukumar sufuri ta jihar (KTSTA).
Gwamnan ya bayyana ta’aziyyarsa ne a wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Asabar ta hannun Malam Ibrahim Kaula, babban sakataren yada labaransa (CPS).
A cewarsa, lamarin wanda ya faru a ranar Juma’a, ya rutsa motar KTSTA mai kujeru 18 da ke hanyar zuwa Abuja daga ofishinsu da ke karamar hukumar Kankara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da hadimin gwamnan ya wallafa a X watau Twitter, Dikko ya kuma bayyana cewa gyare-gyaren da ake yi a babban titin Kaduna zuwa Abuja ne ya haddasa hatsarin.
"Aikin gina sabon titin ne ya sa aka sauya wa ababen hawa hanyar wucewa, masu aiki suka aje abubuwa a kan titin don ishara, bisa tsautsayi suka haddasa hatsarin."
"Abin takaici, an rasa rayuka bakwai, ciki har da yara biyu da direban motar nan take a wurin da hatsarin ya afku," in ji shi.
Gwamna Raɗɗa ya aika sakon ta'aziyya
Gwamna Radda ya nuna kaɗuwarsa da kuma tsayawa bayan iyalan wadanda suka rasu da al'ummar jihar a wannan mawuyacin lokaci.
"A madadin ɗaukacin al'ummar Katsina, ina mai rokon Allah SWT ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu kuma sanya su a gidan Aljannatul Firdausi."
"Gwamnatin jiha ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaron lafiyar mazauna kuma za ta yi aiki tukuru don dakile irin wannan mummunan lamari a nan gaba," in ji Radda.
Yan bindiga sun ƙona kayan ɗakin amare a Katsina
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun bankawa motar da ta ɗauko kayan ɗakin amare uku wuta, sun kashe direba da yaron motar a jihar Katsina.
Ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru a kan titin Jibia zuwa Batsari ranar Talata lokacin da 'yan bindiga suka tare hanyar.
Asali: Legit.ng