Tsohon Mataimakin Sifetan ’Yan Sanda Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Sifetan ’Yan Sanda Ya Magantu
- Babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Olukayode Egbetokun ya sanar da rasuwar tsohon mataimakin Sifetan 'yan sanda
- Egebtokun ya fitar da sanarwar ce a yau Juma'a 12 ga watan Janairu ta bakin kakakin hukumar, ACP Olumuyiwa Adejobi
- Marigayin AIG Okoye Ikemefuna ya rasu a ranar 7 ga watan Janairu bayan fama da jinya na tsawon lokaci da shekaru 68
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Olukayode Egbetokun ya bayyana alhininsa bayan rasuwar tsohon mataimakin Sifetan 'yan sanda.
Marigayin AIG Okoye Ikemefuna ya rasu a ranar 7 ga watan Janairu bayan fama da jinya na tsawon lokaci da shekaru 68, cewar The Nation.
Yan Najeriya sun yi martani yayin da Kotun Koli ke yanke hukunci a zabukan gwamnonin Kano, Filato da Legas
Yaushe marigayin ya rasu?
Egbetokun ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fita a shafin X yau Juma'a 12 ga watan Janairu ta bakin kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Babban Sifetan 'yan sanda, Olukayode Egbetokun ya yi alhini a madadin rundunar 'yan sandan Najeriya kan rasuwar Okoye Ikemefuna.
"Marigayin wanda tsohon mataimakin Sifetan 'yan sanda ne ya rasu a ranar 7 ga watan Janairu.
"Zuciyarmu na tare da iyalan marigayin kuma mun tura sakon ta'aziyya ga abokai da kuma 'yan uwa yayin wannan hali da ake ciki."
Martanin rundunar 'yan sanda?
Egbetokun ya yi addu'ar samun rahama ga marigayin inda ya ce tabbas wannan rashin cike gurbinta zai yi wahala musamman a wannan lokaci da ake ciki.
An haifi Okoye a ranar 15 ga watan Yunin 1955 yayin da ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1984, Blueprint ta tattaro.
Har ila yau, marigayin ya rike mukamin kwamishinan 'yan sanda a jihar Ogun daga shekarar 2010 zuwa 2014.
Fitaccen dan siyasa ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, Fitaccen dan siyasa a jihar Zamfara, M. Z Anka ya riga mu gidan gaskiya a Sokoto.
Marigayin shi ne mahaifin kwamishinar kiwon lafiya a jihar Zamfara, Dakta Aisha M. Z Anka.
Anka ya rasu ne a Sokoto bayan fama da jinya wacce ta dade tare da shi na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng