“Ina Bukatar Karin Mata 5 Don Mafarkina Ya Zama Gaske:” Matashi Ya Nunawa Duniya Matansa 2 a Bidiyo

“Ina Bukatar Karin Mata 5 Don Mafarkina Ya Zama Gaske:” Matashi Ya Nunawa Duniya Matansa 2 a Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya da ke auren mace fiye da daya ya jinjinawa kyawawan matansa biyu yayin da ya nunawa duniya su
  • Matashi ya ce burinsa a duniya shine ya auri mata bakwai, cewa yana bukatar karin mata biyar don cika shi
  • Wani bidiyonsa tare da matansa biyu suna holewarsu ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da mutane suka jinjina masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi dan Najeriya mai suna Obafolarin, ya jinjinawa matansa biyu, Ayomide da Mayowa a dandalin soshiyal midiya.

A wani bidiyon TikTok, matashin mawakin yana ta wasa da su yayin da yake nunawa duniya yadda suke zamansu lafiya a gidan aurensu.

Matashi ya nunawa duniya matansa biyu
“Ina Bukatar Karin Mata 5 Don Mafarkina Ya Zama Gaske:” Matashi Ya Nunawa Duniya Matansa 2 a Bidiyo Hoto: @iam_obaflow
Asali: TikTok
"Matana sun fi dukkan mata a duniya ❤️ @Mummy Batife ❤️ Da @— MAYORWA," ya rubuta.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da za su rungumi jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Allah ya albarkaci aurensu da yara biyu. A cikin wani bidiyon, Obafolarin ya nuna muradinsa na kara wasu matan don cika burinsa na mallakar mata bakwai.

Ya ce sannan za su dunga raba kwana, kowace rana mace daya a bakwai kenan a mako.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun jinjina masa

Real Fish Osha ya yi martani:

"Dan uwa aikinka na kyau."

nomzy ya ce:

"Wannan ne ya auri mata 2 don haka ba za mu ji wani abu ba.
"Lemon da iyalinsa suna nan a soshiyal midiya suna haushi kamar kare."

Roseangie ta ce:

"Daya za ta kashe daya wata rana."

INVESTOR LINK ya ce:

"Kana kokari gaskiya."

Stoic ya ce:

"Kawai ka mallaki kudi. Kudi na hana shirme."

Budurwa ta koka yayin da saurayinta ya auri wata

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano cewa saurayinta ya auri wata daban.

Kara karanta wannan

Zo ka jaraba: Bature na neman yan Najeriya da za su iya yin minti 3 suna kuka, zai biya daloli

A cikin wani bidiyon TikTok, @queensglownaturals ta bayyana cewa sun shafe shekaru bakwai tare, sannan ta bayyana cewa ta sha wahala da shi.

Tana ta sharban kuka a bidiyon yayin da ta mayar da hankali kan kamarar. Ta tuna yadda ta bata lokacinta, karfinta harma da zama da yunwa tare da shi yayin da take tallafawa aikinsa na barkwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng