Ministan Tinubu Na Tsaka Mai Wuya, EFCC Ta Waiwayi Binciken Da Ake Zarginsa Da Wawure N70bn
- Shugaban hukumar EFCC ya yi alƙawarin sake nazari kan binciken Matawalle bisa zargin wawure N70bn daga baitul malin Zamfara
- Ola Olukoyede ya ce zai kakkaɓe fayil din binciken ya dawo ɗanye domin tun da ya fara aiki a EFCC yake duba kesa-kesan da ya gada
- Ya faɗi haka ne ta bakin daraktan hulɗa da jama'a na EFCC yayin zanga-zangar wata ƙungiya a hedkwata da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya sha alwashin sake tado da binciken karamin ministan tsaro, Bello Matawalle kan zargin karkatar da kudi N70bn.
Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, shugaban EFCC ya lashi takobin bankaɗo fayil ɗin binciken Matawalle tare da sake nazari kan kes din badaƙar kuɗin lokacin yana gwamnan Zamfara.
Mista Olukoyede ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu 2023 ta bakin daraktan hulda da jama’a na EFCC, Wilson Uwujaren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ɗauki alkawarin sake buɗe kundin binciken karkatar N70bn ne biyo bayan zanga-zangar da wata ƙungiya 'Zamfara Alternative Forum' ta yi a hedkwatar EFCC da ke Jabi a Abuja.
Mambobin kungiyar sun mamaye hedikwatar EFCC ranar Juma’a don nuna rashin jin daɗinsu, kana suka buƙaci hukumar ta sake nazari kan binciken Matawalle.
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, mai magana da yawun kungiyar, Mahmud Abubakar, ya bukaci hukumar EFCC da ta ci gaba da binciken tsohon gwamnan.
Zamu yi nazari kan badaƙalar Matawalle - EFCC
A rahoton Leadership, yayin da yake martani kan zanga-zangar, Uwujaren ya ce:
"Mun gode wa kungiyar Zamfara Alternative Forum da ta yi hakan cikin lumana. Muna son irin wannan zanga-zangar lumana da yunkurin matasan, ina tabbatar muku da cewa a EFCC babu wanda ya fi karfin doka.
"Tun da shugaban hukumar EFCC ya kama aiki ya fara nazari da bankaɗo manyan kes ɗin da ya gada kuma ya ce na baku tabbacin cewa kes din da kuke ƙorafi ba zai zama shafaffe da mai ba.
"Za a sake duba lamarin, kuma shugaban EFCC na tabbatar muku da cewa za a yi wani abu bisa tanadin doka domin babu wanda ya fi karfin doka."
Matawalle ya yi rashin nasara a kotun ƙoli
A wani rahoton kuma kun ji cewa Bello Matawalle na APC ya sha kaye hannun Gwamna Lawal na PDP a hukuncin kotun koli.
Mai shari'a Agim, wanda ya jagoranci yanke hukuncin ya ce ɗan takarar APC, Bello Matawalle, ya gaza gamsar da kotu kan ikirarinsa.
Asali: Legit.ng