Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Bauchi
- A karshe dai Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi
- Kotun ta ce hujjojin da jam'iyyar APC da dan takararta Sadique Abubakar suka gabatar ba su da makama
- Hakan na nufin Kotun Kolin ta bi sahun Kotun Daukaka Kara da kotun sauraron kararrakin zaben wajen tabbatar da nasarar Mohammed
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Rahotan da Legit Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Bala Mohammed matsayin gwamnan jihar Bauchi.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da APC da dan takararta Sadique Abubakar suka shigar na kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da na kotun sauraron kararrakin zaben jihar Bauchi.
Gwamna Bala ya yi magana kan samun nasara a Kotun Koli
Kotun ta tabbatar da sakamakon kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), tare da yin watsi da karar da Abubakar ya yi na rashin cancantar ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jim kadan bayan sanar da sakamakon kotun, Gwamna Bala Mohammed ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya yi wa Allah godiya kan wannan nasarar.
Mu waiwaya baya
A watan Maris na 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Bauchi.
Daga nan Abubakar ya garzaya kotun domin kalubalantar sakamakon zaben, jaridar The Cable ta ruwaito.
A watan Satumban 2023, kotun ta yi watsi da karar da Abubakar da APC suka shigar.
A watan Nuwamba 2023, kotun daukaka kara ta tabbatar da Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.
Kotun koli ta fara karin kumallo da shari'ar gwamnan Legas
A safiyar yau Legit Hausa ta ruwaito maku yadda Kotun Koli ta fara sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Legas, tsakanin LP, PDP da jam'iyyar APC mai mulki.
Sai dai a hukuncin da ta yanke, kotun ta tabbatar da cewa Gwamna Babajide Samwo-Olu ne ya lashe zaben gwamna jihar ta Legas.
Asali: Legit.ng