Betta Edu: Gwamonin APC Sun Dauki Mataki Ana Tsaka da Binciken Badakala, Bayanai Sun Fito

Betta Edu: Gwamonin APC Sun Dauki Mataki Ana Tsaka da Binciken Badakala, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun tsoma baki a takaddamar da ke kewaye da badakalar Dr Betta Edu
  • Ana dai bincikar Ministar jin kai da kawar da talauci da aka dakatar bisa karya dokar kayyade kudi ta 2009
  • Da yake magana a madadin gwamnonin APC, gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma ya ce babu bukatar yin hayaniya kan zargin da ba a tabbatar da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Kungiyar gwamnonin APC ta shawarci jama'a da su guji gaggawar yanke hukunci kan zargin rashawa da ake yi wa Betta Edu, dakatacciyar ministar jin kai da kawar da talauci.

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, wanda ya jagoranci kungiyar ta PGF, ya yi jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, bayan wani taron kungiyar.

Kara karanta wannan

Betta Edu: EFCC ta bugi ruwan cikin manyan jami’ai 10 na ma’aikatar jin kai, bayanai sun fito

Gwamonin APC sun nemi a daina gaggawar yanke hukunci kan zargin da ake yi wa Betta Edu
Betta Edu: Gwamonin APC sun dauki mataki ana tsaka da binciken badakala, bayanai sun fito Hoto: EFCC/Dr Betta Edu
Asali: Twitter

Da yake jawabi ga manema labarai, Gwamna Uzodimma ya shawarci yan Najeriya da su daina yanke hukunci har sai an kammala binciken da ake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto, Gwamna Uzodimma ya jaddada cewa aikin gwamnati ya hada da inganta ayyuka masu kyau da kuma yaba ma masu mukamai na kwarai.

Haka kuma yana daga cikin aikin gwamnati hana ayyukan da ba su dace ba da kuma tsawatarwa masu mukamai da suka saba.

Ya kuma jadadda cewa ya kamata a ci gaba da daukar zargin da ake yi wa Ms Edu a matsayin zargi kawai.

Gwamna Uzodimma ya ce:

“Kuma bisa hikimar shugaban kasa, ana bincike kanta. Bayan an kammala bincike tare da gabatar da rahoton ga gwamnati lokacin ne za ta yanke hukuncin karshe.”

An roki yan Najeriya su yafe ma Edu

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa Femi Pedro, tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, ya roki ƴan Najeriya da su sake baBetta Edu, ministar ayyukan jin ƙai da yaƙi da talauci da aka dakatar, dama a karo na biyu.

Tsohon mataimakin gwamnan na jihar Legas a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za ta koyi darasi mai zurfi daga kura-kuran da ta yi, sannan ta yi abin da ya dace nan gaba, cewar rahoton jaridar TheCable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng